APC ta mika sakon ta'aziyya ga PDP bisa rasuwar mambobinta da su kayi hatsarin mota

APC ta mika sakon ta'aziyya ga PDP bisa rasuwar mambobinta da su kayi hatsarin mota

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta mika sakon ta'aziya ga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bisa rasuwar mambobinta da su kayi hatsarin mota a titin Otukpo-Agatu na jihar Benue.

Mambobin na jam'iyyar PDP suna kan hanyarsu na zuwa kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Sanata ne a ranar Juma'a yayin da hatsarin ya afku.

Mai magana da yawun APC, Mallam Lanre Issa-Onilu ya ce tana cike da alhini da juyaya kan abin bakin cikin da ya faru.

APC tayi ta'aziyar magoya bayan jam'iyyar PDP da suka rasu

APC tayi ta'aziyar magoya bayan jam'iyyar PDP da suka rasu
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

"A yayin da muke taya wadanda suka rasa 'yan uwansu bakin ciki, muna addu'ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

"Muna rokon Allah ya jikan wadanda suka rasu ya saka musu da gidan aljanna kuma ya bawa iyalansu ikon jure wannan babban rashin."

Mai magana da yawun na APC ya yi kira ga dukkan jam'iyyun siyasa su kiyaye lafiyar mambobinsu musamman a yanzu da babban zaben shekarar 2019 ke karatowa.

"Muna kuma kira ga dukkan hukumomin da ke kula da tituna da filayen kaddamar da yakin neman zabe su tabbatar da cewa sunyi shirin da ya dace domin tabbatar da kiyaye lafiyar al'ummar tare da kare afkuwar sauran haddura," inji Issa-Onilu.

An ruwaito cewar kimanin mutane 12 ne suka rasu a hatsarin motan da ya afku a jihar ta Benue.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel