Babban Bankin kasa, CBN, ya tilastawa bankuna karbar kukan kwastomomi da korafi

Babban Bankin kasa, CBN, ya tilastawa bankuna karbar kukan kwastomomi da korafi

- Babban bankin Najeriya ya kirkiro da bangaren karbar korafi a duk bankunan fadin kasar nan

- Yayi hakan ne don saukake matsalolin da mutane ke fuskanta da bankuna da sauran ma'aikatun kudi

- Rashin bin dokokin ga bankuna zai jawo fuskantar hukunci

Babban Bankin kasa, CBN, ya tilastawa bankuna karbar kukan kwastomomi da korafi

Babban Bankin kasa, CBN, ya tilastawa bankuna karbar kukan kwastomomi da korafi
Source: Depositphotos

Babban bankin Najeriya ya kirkiro da cibiyar sauraren korafe korafe a bankuna don saukake shawo kan matsaloli.

Bankin ya bayyana hakan ne a takardar da ya fitar a shafin shi ta yanar gizo a ranar juma'a, cewa bangaren anyi shi ne don saukin sauraren korafi.

Bangaren zai karawa yan Najeriya karfin guiwa a bangaren bankunan kasar nan.

Bankin yace hakan na daga cikin aikin bankin kolin wajen tabbatar da cewa bangaren kudin kasar nan ya zama daidaitacce.

"Babban bankin Najeriya ya tabbatar da cewa alhakin shi ne wajen tabbatar da daidaitaccen cigaba ta bangaren kudi don haka ne ya kirkiro CCMS. A saboda hakan ne babban bankin Najeriya ya wajabtawa duk wasu bankunan kasar nan da su tsare dokoki uku.

Dole ne bankuna su maida hankali akan duk wani korafi da ma'abota amfani da bankin suka kawo.

Akwai bukatar bankuna su tabbatar da sun karbi korafi ta hanyar tura sako ga mai korafin ta yanar gizo.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya mazauna Indiya dake kurukuku a can na kira ga gwamnati da ta jiyo kukansu

Hakan zai hada gano lambar da aka bada a korafin tare da tura duk korafe korafen ga CCMS."

Babban bankin ya shawarci bankuna da su tabbatar sun bi wadannan dokokin da za'a fara amfani da su a 2 ga watan janairu,2019.

Ya kara da cewa, "Rashin bin dokokin nan zai jawowa bankin fuskantar hukunci daga cikin hukunce hukunce bankuna da ma'aikatun kudi."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel