Ina dalilin Buhari da bai kaddamar da yakin neman zaben sa ba a jihar Zamfara, Yobe ko Borno - Fayose

Ina dalilin Buhari da bai kaddamar da yakin neman zaben sa ba a jihar Zamfara, Yobe ko Borno - Fayose

A yayin da tsagwaran adawa ta siyasa ke ci gaba da kai komo a zuciyar tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya nemi dalilin da ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kaddamar da yakin neman zaben sa ba a daya daga cikin jihohin Zamfara, Yobe ko Borno.

Mun samu cewa, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya na mamaki dangane da dalilan da ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kaddamar da kaddamar da yakin neman zabensa ba a daya daga jihohi Zamfara, Yobe da kuma Borno.

Ko shakka ba bu, a jiya Juma'a, shugaban kasa Buhari ya dira a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda ya kaddamar da yakin neman zaben sa gadan-gadan domin tumke damararsa yayin da babban zaben kasa na 2019 ya gabato.

Buhari yayin kaddamar da yakin neman zaben sa a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom

Buhari yayin kaddamar da yakin neman zaben sa a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom
Source: UGC

Lamarin ya sanya tsohon gwamnan ya bayyana takaicin sa a shafin sa na zauren sada zumunta, inda ya ke cewa rayukan al'ummar Najeriya na ci gaba da salwanta a jihar Zamfara amma shugaba Buhari bai ko iya kai ma su ziyara domin jajantawa sai dai ya kiraye su ta wayar salula.

Ga sakon kamar haka:

Fayose ya ce ba bu dalilin Buhari na kaddamar da yakin neman zaben sa a jihar Akwa Ibom da jagorancin gwamnatin jam'iyyar PDP ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali karkashin kulawar gwamna Emmanuel Udom.

KARANTA KUMA: Buhari, Saraki da sauran jiga-jigan Najeriya sun yi bakin cikin rasuwar Marigayi Shagari

Cikin rubutaccen sakon da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta na Twitter, Fayose ya ce ina dalilin da shugaban kasa Buhari bai kaddamar da yakin neman zaben sa ba a jihar Zamfara, Yobe ko Borno?

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tun a ranar Talatar da ta gabata shugaban kasa Buhari ya yi subul da bakan kaddamar da yakin neman zaben sa a jihar dake karkashin gwamnatin jam'iyyar adawa ta PDP.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel