Buhari, Saraki da sauran jiga-jigan Najeriya sun yi bakin cikin rasuwar Marigayi Shagari

Buhari, Saraki da sauran jiga-jigan Najeriya sun yi bakin cikin rasuwar Marigayi Shagari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana babban baƙin cikin sa dangane da rasuwar tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari, da ya riga mu gidan gaskiya a jiya Juma'a bayan fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya.

Shugaban kasar yadda ya hikaito da sanadin kakakin sa, Mista Femi Adesina, ya bayyana yadda rayuwar tsohon shugaban kasar ta dawwama akan kishin kasar sa ta Najeriya gami da kana'a, tawakkali da kuma kyawawan dabi'u da ba za su misaltu ba.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaba Buhari ya zayyana yadda Marigayi Shagari ya ci moriyar rayuwarsa cikin tabarraki da ko shakka ba bu ya yi shimfidar ababen koyi da a halin yanzu gargadin al'ummar Najeriya da su bibiyi tafarkin sa.

Marigayi Alhaji Shehu Shagari

Marigayi Alhaji Shehu Shagari
Source: UGC

Kazalika shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana baƙin cikin sa dangane da rasuwar tsohon shugaban kasar, inda ya misalta shi a matsayin babban gwarzo da ya sadaukar da rayuwarsa kan tafarkin tabbatar da zaman lafiya da yiwa Najeriya hidima.

Da yawan jigan-jigan sun bayyana baƙin cikin su kwarai da aniyya dangane da rasuwar tsohon shugaban kasar, inda suka kwarara yabo gami da jinjina akan mafi kyawun rayuwa da ya kasance a kai tare da rokon mai duka ya jikan sa da rahama.

KARANTA KUMA: Buhari: Za mu kara tsanani akan yaki da rashawa daga 2019

Ire-iren jiga-jigan kasar sun hadar da; Sanata Shehu Sani, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Sanata Ike Ekweremadu, James Onafefe Ibori, Mista Godwin Obaseki, Peter Obi, Goodluck Jonathan, Ibikunle Amosun, Nyesom Wike da makamantan su.

Maruwaita tarihi sun bayyana cewa, Marigayi Shagari ya mulki kasar nan a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983. An haife sa a shekarar 1925 kuma ajali ya cimmasa yana mai shekaru 93 a duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel