Adadin mutanen da EFCC ta gurfanar a kowacce jiha a 2018

Adadin mutanen da EFCC ta gurfanar a kowacce jiha a 2018

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bugi kirjin cewar ta gurfanar da kimanin mutane 312 da ta kama a kan aikata laifukan cin hanci da rashawa a tsakanin watan Janairu da ranar 24 ga watan Disamba na shekarar 2018.

A sanarwar da ta fitar ta bakin kakakinta, Tony Orilade, EFCC ta ce ta samu gagarumar nasara idan aka kwatanta da adadin mutane 189 da ta gurfanar a shekarar 2017.

Sanarwa ta ce, "mafi muhimmanci shine kasancewar tsofin gwamnoni biyu daga cikin mutanen da muka gurfanar, wadanda yanzu haka suna gidan yari bayan kotu ta yanke masu hukunci. Akwai babban lauya, Joseph Nwobike, da hukumar EFCC ta janyo ya rasa lasisinsa na aikin lauya bayan samun sa da laifin kokarin dakile hukuncin kotu.

Adadin mutanen da EFCC ta gurfanar a kowacce jiha a 2018

Adadin mutanen da EFCC ta gurfanar a kowacce jiha a 2018
Source: Facebook

"Da wadannan nasarori da EFCC ta samu karkashin jagorancin Ibrahim Magu, hukumar ta tabbatar da ikirarinta na yaki da cin hanci domin inganta tsarin gudanar da gwamnati a Najeriya.

"EFCC ta samu wannan nasara ne a ofisoshinta dake fadin kasar nan.

DUBA WANNAN: Fusataccen gwamnan APC ya bayyana dalilin canjin shekar magoya bayansa

Da take fashin baki a kan wadannan alkaluma, EFCC ta ce ofishinta na Legas ya gurfanar da mutane 85, mutane 53 a ofishinta na Abuja, sai na jihar Kano da ya gurfanar da mutane 36. An gurfanar da mutane 33 a ofishin EFCC na Fatakwal, 28 a ofishin Gombe, 27 a Benin, 15 a Enugu, 11 a Maiduguri, Ibadan mutane 10, 8 a Uyo, sai kuma mutane 8 a Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Jerin mutanen da EFCC ta gurfanar a kowacce jiha a 2018

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel