Yadda hukumar sojin sama suka yiwa yan Boko Haram ruwan wuta a Baga (Bidiyo)

Yadda hukumar sojin sama suka yiwa yan Boko Haram ruwan wuta a Baga (Bidiyo)

Hukumar sojin saman Najeriya ta sakin faifan bidiyon yadda da hallaka dimbin yan kungiyar Boko Haram cikin kwanaki biyu da suka gabata a garin Baga, jihar Borno bayan yan ta'addan sunyi kokarin kwace barikin sojojin MNJTF.

Kakakin hukumar, Ibikunle Daramola, ya saki jawabi tare da faifan bidiyon inda yayi bayani filla-filla kan abin da ya faru sabanin abubuwan da kafafen yada labarai ke wallafawa.

Jawabin yace: "Za ku tuna cewa hedkwatan rundunar 7 Brigade na dakarun MNJTF dake Baga ta fuskanci hari daga yan kungiyar daular musulunci a Afrika ta yamma wato ISWAP da yammacin ranan 26 ga watan Disamba 2018.

"Yayinda muka samu wannan labari, rundunar sojin saman Operation Lafiya Dole ta tura jami'anta tare da jirage masu saukar angulu na Mi-35M domin taimakawa soji wajen dakile yan ta'addan."

"Jami'an hukumar sojin saman sunyi aiki hannu da hannu da na hukumar sojin kasa domin budewa yan ta'addan wuta, yayinda jirgi mai saukar angulu ke kashe yan ta'addan a wuraren da babu jama'a inda suka hallaka wasu daga cikinsu"

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: Dino Melaye ya boye cikin gidansa, yan sanda sun shiga tsamoshi

Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar Sojin Najeriya ta ce ba gaskiya bane cewa mayakan Boko Haram sun kwace garin Baga duk da cewa har yanzu ana gwabzawa tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a garin.

Shugaban bayar da horo da ayyuka na soji, Manjo Janar Lamidi Adeosun ne ya bayarda wannan sanarwar a taron manema labarai da ya kira a hedkwatan Operation Lafiya Dole a Borno.

Wannan sanarwar ta hukumar sojin yana zuwa ne a lokacin da wasu rahotanni ke yaduwa na cewa mayakan kungiyar Boko Haram na sashin Albarnawi sun kwace garin Baga a jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel