Na isar da alkawaran zaben da na dauka, ba za ku yi danasanin zaben APC ba a 2019 - Buhari

Na isar da alkawaran zaben da na dauka, ba za ku yi danasanin zaben APC ba a 2019 - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari yace ya isar da alkawaran zabensa duk da kokwanton da jam’iyyar adawa ke yi

- Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da kamfen dinsa a Uyo, babbar birnin Akwa Ibom

- Buhari ya yi alkawarin cewa yan Najeriya ba za su yi danasanin sake zabar ba a 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ya isar da alkawaran zabensa duk da kokwanton da jam’iyyar adawa ke yi.

Buhari ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba a Uyo, babbar birnin jihar Akwa Ibom yayinda jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ta kaddamar da kamfen dinta a yankin kudu-maso-kudu.

A cewarsa, yan Najeriya ba za su yi danasanin zabar yan takarar APC ba a 2019.

Na isar da alkawaran zaben da na dauka, ba za ku yi danasanin zaben APC ba a 2019 - Buhari

Na isar da alkawaran zaben da na dauka, ba za ku yi danasanin zaben APC ba a 2019 - Buhari
Source: UGC

Yace ya isar da alkawarin da ya daukar ma yan Najeriya ta fannin tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Shugaban kasar yace koda dai Boko Haram ya kasance kalubale a wasu yan kunan kasar, tsaron da aka tura domin maganinsu za su yi kasa-kasa da su.

KU KARANTA KUMA: Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari

Ya kuma bayyana cewa koda dai rashin aikin yi shine babban kalubalen Najeriya, gwamnatin nan na aiki domin magance matsalar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tabbatar da tsaron abinci da kuma karfafawa manoman Najeriya gwiwa domin cimma tsaron abinci.

Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yakar cin hanci da rashawa idan har aka zabe shi karo na biyu a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel