Zaben 2019: Buhari zai dasa sabon gini ne – Tinubu

Zaben 2019: Buhari zai dasa sabon gini ne – Tinubu

Babban jigon jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai dasa wani sabon gini ne ga matasa da dattawan Najeriya.

A wajen kamfen din shugaba Buhari da aka kaddamar a Uyo, Tinubu ya bukaci matasa da su zabe shugaban kasar don makomarsu na gaba.

Tinubu yayi bayanin cewa tsawon shekaru 16, PDP tayi tana gina Najeriya akan cin hanci da rashawa da kuma duhu.

Ya bayyana cewa APC ta daidata Najeriya sannan ta jajirce wajen habbaka tattalin arziki.

Zaben 2019: Buhari zai dasa sabon gini ne – Tinubu

Zaben 2019: Buhari zai dasa sabon gini ne – Tinubu
Source: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana cewa APC ta zo mulki a lokacin da ýan Najeriya ke tsananin bukatar chanji, chanji daga lalaci.

Adams Oshiomhole, shugaban APC na kasa, a gajeren jawabi da yayi ya bayyana cewa a sa’o’i 48 da suka shige, PDP na ta kokatin bata sunan shugaba Buhari amma yayi bayanin cewa yan Najeriya sun san wanene Buhari annan sun san wanene PDP.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ba mu da masaniya akan mamayar da aka kai gidan Dino – Yan sanda

Yace dan takarar PDP ba zai iya Magana a wasu yankunan duniya ba amma Buhari babu inda ba zai shiga yayi Magana ba.

Ya roki mutanen kudu maso kudu da kada su zabi PDP saboda Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar yayi alkawarin siyar da NNPC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel