ASUU: Watakila ba za ayi amfani da ‘Dalibai a 2019 ba – INEC

ASUU: Watakila ba za ayi amfani da ‘Dalibai a 2019 ba – INEC

Hukumar zabe na kasa watau INEC ta bayyana cewa watakila ba za tayi amfani da ‘Daliban makaranta a wajen gudanar da zaben 2019 ba saboda yajin aikin da Malaman jami’o’i su ke yi a kasar nan.

ASUU: Watakila ba za ayi amfani da ‘Dalibai a 2019 ba – INEC

Hukumar INEC tace yajin aikin Jami'o'i zai iya kawo cikas
Source: Depositphotos

Yajin aikin da ASUU su ke yi yana yi wa hukumar INEC barazana inji Musa Muhammad Sokoto, wanda shi ne shugaban wayar da kan jama’a game da zabe a hukumar INEC, ya bayyanawa jama’a wannan a wajen wani taro.

Alhaji Musa Muhammad Sokoto yake cewa dole INEC ta nemi mutanen da za su yi aikin wucin-gadi a zaben 2019 saboda yajin aikin da ake yi a Jami’o’in Najeriya. Yanzu haka dai jami’o’in kasar su na rufe na makonni.

KU KARANTA: ‘Yar takarar ACPN ta shiga yakin neman zabe gadan-gadan

Akwai bukatar hukumar INEC ta dauki hayar ma’aikata 16, 000 domin a gudanar da zaben 2019. Rufe makarantun kasar da aka yi ne ya sa hukumar INEC ta shiga halin kila-wa-kala a zaben da za ayi a farkon shekarar badi.

INEC ta saba daukar ‘Daliban da ke jami’a da masu hidimar kasa na NYSC a matsayin ‘yan wucen-gadi. Haka kuma a kan dauki manyan Farfesoshin jami'an a matsayin malaman da ke sanar da zabe tun bayan 2011 a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel