Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Alhaji Shehu Shagari rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Alhaji Shehu Shagari rasuwa

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Rahoton da ke shigo mana yanzu daga hannun babban hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, na nuna cewa Allah ya yiwa tsohon shugaban kasan Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, rasuwa.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na Tuwita da yammacin Juma'a misalin karfe 7:30.

Alhaji Shehu Shagari ya rasu ne bayan jinya a wata asibiti dake birnin tarayya Abuja. Alla ya karbi ransa yana mai shekaru 93 da haihuwa.

Marigayin ya kasance zababben shugaban kasan Najeriya na farko na mulkin demokradiyya kuma ya mulki Najeriya daga shekarar 1979 zuwa 1983 kafin akayi masa juyin mulki.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel