Yanzu Yanzu: Ba mu da masaniya akan mamayar da aka kai gidan Dino – Yan sanda

Yanzu Yanzu: Ba mu da masaniya akan mamayar da aka kai gidan Dino – Yan sanda

- Hukumar yan sandan Najeriya ta karyata batun kai farmaki gidan Dino Melaye

- Da farko mun ji yadda wasu jami’an yan sanda suka mamaye gidan Melaye na Abuja a yau

- Dino dai ya yi zargi cewa Ibrahim Idris, Sufeto Janar na yan sanda yayi umurnin a kama shi ayi masa alluran mutuwa

Rundunar yan sandan Najeriya ta karyata kai farmaki gidan Dino Melaye, Sanata mai wakiltan Kogi ta yamma.

Daga kakakin rundunar yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, har kakakin yan sandan birnin tarayya, Manzah Anjuguri, sun bayyana cewa basu da masaniya akan farmakin.

Yanzu Yanzu: Ba mu da masaniya akan mamayar da aka kai gidan Dino – Yan sanda

Yanzu Yanzu: Ba mu da masaniya akan mamayar da aka kai gidan Dino – Yan sanda
Source: UGC

Da farko mun ji yadda wasu jami’an yan sandan suka kai mamaya gidan Dino Melaye na Abuja a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba.

Lamarin ya faru kwanaki uku bayan sanatan yayi zargin cewa Ibrahim Idris, Sufeto Janar na yan sanda yayi umurnin a kama shi ayi masa alluran mutuwa.

KU KARANTA KUMA: Hutun Kirsimeti: Ma’aikata sun yi kaura a majalisar dokokin tarayya duk da cewar hutu ya kare

Da farko sun kai mamaya unguwar Sangha da ke kusa da Mississippi, Maitama inda gidan dan majalisan yake kafin su samu shiga harabar gidansa.

Amma rundunar yan sanda ta karyata sanin masaniya akan mamayar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel