Badakalar WAEC: Dalilin da yasa bamu cafke hadimin Buhari ba - Rundunar 'yan sanda

Badakalar WAEC: Dalilin da yasa bamu cafke hadimin Buhari ba - Rundunar 'yan sanda

- Rundunar 'yan sanda ta maida martani kan bukatar da majaliar wakilan tarayya na cafke wani hadimin Buhari akan zarginsa da amfani da takardun WAEC na bogi

- Majalisar wakilan tarayya ta bukaci Ibrahim Idris, da ya cafke Okoi Obono-Obla tare da hukunta shi, sakamakon zargin da take masa

- Hadimin shugaban kasar, yayi amfani da takardar WAEC din da ake zargin ta bogi ne, wajen yin karatu a jami'ar Jos, da shiga makarantar lauyoyi ta Nigeria

Rundunar 'yan sanda ta maida martani kan bukatar da majaliar wakilan tarayya ta gabatar na cafke wani hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zarginsa da amfani da takardun WAEC na bogi.

A cikin wata tattaunawa da jaridar TheCable, Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sandan, ya ce wannan bukata ta cafke Okoi Obono-Obla, babban hadimin Buhari a fuskar yanke hukunci, ta gaza samun tagomashi saboda ba a shigar da kara ta musamman ga rundunar ba.

Majaisar wakilan tarayya ta bukaci Ibrahim Idris, Sifeta Janar na rundunar 'yan Sanda, da ya cafke tare da hukunta hadimin shugaban kasar, sakamakon zarginsa da mallakar takardar jarabawar WAEC ta bogi.

KARANTA WANNAN: Mutumin da yafi dacewa ya kawo karshen cin hanci da ta'addanci shine Buhari - Bajowa

Badakalar WAEC: Dalilin da yasa bamu cafke hadimin Buhari ba - Rundunar 'yan sanda

Badakalar WAEC: Dalilin da yasa bamu cafke hadimin Buhari ba - Rundunar 'yan sanda
Source: Twitter

Hadimin shugaban kasar, wada yayi amfani da takardar WAEC din da ake zargin ta bogi ne, wajen samun gurbin karatu a jami'ar Jos, har ila yau yayi amfani da takardar wajen shiga makarantar lauyoyi ta Nigeria.

Sai dai, ba asake jin tashin zancenba tun bayan da majalisar wakilan ta gabtarwa rundunar 'yan sanda wannan bukata.

Ko da aka bukace shi yayi jawabi akan wannan lamari a ranar Juma'a, Moshood ya shaidawa TheCable cewa rundunar bata samu wani korafi kai tsaye daga majalisar tarayyar ba kan wannan bukata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel