Mutumin da yafi dacewa ya kawo karshen cin hanci da ta'addanci shine Buhari - Bajowa

Mutumin da yafi dacewa ya kawo karshen cin hanci da ta'addanci shine Buhari - Bajowa

- Manjo Janar Oluyemi Bajowa (mai ritaya) ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne yafi dacewa ya sake shugabantar kasar a 2019

- Bajowa ya ce idan aka sake baiwa Buhari damar sake shugabantar kasar zai magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma kashe kashen rayuka da ake yi

- Bajowa ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, a cikin wani sako da ya aikewa 'yan Nigeria a bukin murnar cikarsa shekaru 78 a duniya

Manjo Janar Oluyemi Bajowa (mai ritaya) ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne yafi dacewa ya sake shugabantar kasar a 2019, wanda zai iya magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma kashe kashen rayuka da ake yi a kasar.

Bajowa ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, a cikin wani sako da ya aikewa 'yan Nigeria a bukin murnar cikarsa shekaru 78 a duniya.

"Muna bukatar shugaba Buhari ya sake dawowa don yaki da cin hanci da rashawa a kasar. Haka zalika kokrinsa na dakile ta'addancin mayakan Boko Haram da kuma shirye shiryen bunkasa rayuwar matasa ya nuna cancantarsa na sake zarcewa a 2019," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Rundunar soji ta fara atisayen rawar Mesa a fadin Nigeria

Mutumin da yafi dacewa ya kawo karshen cin hanci da ta'addanci shine Buhari - Bajowa

Mutumin da yafi dacewa ya kawo karshen cin hanci da ta'addanci shine Buhari - Bajowa
Source: UGC

Bajowa, wanda shine Agunmolu na kasar Ikale, da ke jihar Ondo, ya bukaci masu kad'a kuri'a a su alkinta katin zabensu tare da gujewa 'yan siyasa masu sayen kuri'u, da kuma 'yan siyasar da ka iya jefa rayuwarsu cikin gagari bayan darewa a karagar mulki.

Ya yi nuni da cewa a cikin shekaru 3 da rabi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna dattakonsa, amanarsa da kuma sha'awar ci gaban Nigeria a zuciyarsa. Yana mai tuna lokacin da yayi aiki da Buhari a matsayin jami'in soji, wanda ke yin komai don rike mutuncinsa.

"Na yi aiki da shi (Buhari) na tsawon shekaru 4 a lokacin ina da mukamin Adjuntant Janar na rundunar soji, don haka nayi masa farin sani. Zan iya bada shaida akan cewa Buhari mutum ne mai mutunci.

"Yana da amana kuma shi mutum ne mai dattako akan gaskiya da son hadin kan jama'a, musamman ma idan aka zo fagen bunkasa tattalin arzikin kasa da rayuwar jama'a," a cewar janar na rundunar sojin mai ritaya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel