Shehu Sani yi martani bayan ikirarin cewa iyalan Buhari na da hannun jari a kamfanoni 2

Shehu Sani yi martani bayan ikirarin cewa iyalan Buhari na da hannun jari a kamfanoni 2

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Shehu Sani ya mayar da martani ga hatsaniyar siyasa tsakanin kungiyoyin kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari da na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Sani, tsohon dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayar da shawarar cewa domin kawo karshen wannan zarge-zarge daga Atiku da kuma martani daga fadar shugaban kasa, kamfanonin biyu su fito da wani jawabi da zai rabar gardama akan lamarin.

Shehu Sani yi martani bayan ikirarin cewa iyalan Buhari na da hannun jari a kamfanoni 2

Shehu Sani yi martani bayan ikirarin cewa iyalan Buhari na da hannun jari a kamfanoni 2
Source: UGC

“Duba ga kurar da ya taso na alamar tambayoyi akan kamfanoni biyu da ake yi,” yace, kamfanonin biyu su wallafa cikakken sunayen masu hannun jari a cikinsu domin kore duhun da ke yawo a sararin samaniyar kasarmu.”

KU KARANTA KUMA: Yari ya kwace min hakkokina – Mataimakin gwamna

A baya mun ji cewa Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta fara bincike kan mamallakan babban kamfanin sadarwa na Etisalat Nigeria da kuma bankin Keystone.

A cikin wata sanarwa, wacce Phrank Shaibu, daya daga cikin hadimansa ya rabawa manema labarai a madadinsa, Atiku ya ce kiran ya zama wajibi ne biyo bayan rahotannin da ke yawo na cewar wasu daga cikin iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari na da hannun jari mai tsoka a Etisalat Nigeria, da suka kai kimanin $2bn.

Shuaibu ya kalubalanci mahukunta da su gudanar da kwakkwaran bincike kan wannan zargi, kana su bayyanawa jama'a sakamakon binciken nasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel