Titi Atiku ta farfado da ayyukanta na jin kai, WOTCLEF ta dawo kan aiki

Titi Atiku ta farfado da ayyukanta na jin kai, WOTCLEF ta dawo kan aiki

- Kungiyar yaki da safarar mutane ta shawarci yan Najeriya da su sa ido don gudun fadawa tarko

- Kungiyar taimakon Kai da kan tana ceto mutane daga yan safara tare da sanyasu makaranta ko koyon sana'a

- Mutanen dake safara suna tare da mu kuma sukanyi amfani da sakacin iyaye

Titi Atiku ta farfado da ayyukanta na jin kai, WOTCLEF ta dawo kan aiki

Titi Atiku ta farfado da ayyukanta na jin kai, WOTCLEF ta dawo kan aiki
Source: UGC

Kungiyar yaki da safarar mata da yara ta shawarci yan Najeriya dasu sa ido don gudun fadawa tarkon masu safarar.

Zababben daraktan kungiyar taimakon kai da kan,Imabong Sanusi ta bada shawarar a wata tattaunawa da tayi da ofishin dillancin labarai a ranar juma'a a Abuja.

Mrs Sanusi tace masu safarar mutane suma mutane ne dake rayuwa tare damu kuma suke amfani da gibin rashin kular iyaye.

Tace za'a iya magance matsalar je kawai idan ana tattauna ta da mutane domin wayar da kai.

"Yan Najeriya su saka ido kuma su guji safarar mutane. Masu safarar mutane suma mutane ne dake rayuwa tare da mu. Suna amfani da rashin kular iyaye ne don jan hankalin wadanda ke fadawa tarkon su. Suma samun kudi ne ta hanyar wadanda suke yaudara. Don haka dole iyaye su sanya ido tare da kula da yayayensu," Mrs Sanusi ta jajanta.

Ta kara da cewa WOTCLEF ta shirya cibiyar binciken safarar mutane da cibiyoyin koyon sana'a don gyara rayuwar mutane.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

"Mutanen da ake safara yawanci akan sanya su karuwanci, wasu a cire musu sassa na jikin su ko kuma dai su fada munanan wahalhalu. A WOTCLEF, mukan ceto wadanda akayi safarar su tare da maida su makaranta ko kuma su koyi sana'a. Muna da hadin guiwa ne da makarantu da wasu wuraren koyon sana'a. A halin yanzu, muna da kusan mutane 30 da muka ceto, biyar daga ciki suna jami'a kuma muna da burin yin fiye da hakan," tayi bayani.

Ta hori yan Najeriya dasu kai rahoton duk wani matsalar tsangwama ko takura ga yara ga hukumomi don daukar mataki.

Mrs Titi Atiku ce ta kirkiro Kungiyar WOTCLEF a shekarar 1999 don kawo karshen matsalar safarar mutane a Najeriya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel