Ganduje na sauye-sauye a gwamnatinsa ana dab da gama zabe

Ganduje na sauye-sauye a gwamnatinsa ana dab da gama zabe

- Gwamnan jihar Kano ya Mika sunayen mutane hudu da yake son nadawa kwamishinoni

- An kara da wata wasikar bukatar amincewar majalisar jihar don yin sabuwar makarantar kiwon lafiya, kimiyya da fasaha

- Majalisar ta bukaci mutanen da ya zaba dasu bayyana gabanta a ranar litinin don tantancewa

Ganduje na sauye-sauye a gwamnatinsa ana dab da gama zabe

Ganduje na sauye-sauye a gwamnatinsa ana dab da gama zabe
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya tura wasika ga majalisar jihar Kano don neman izinin zabar kwamishinoni hudu da Odita janar na jihar.

Kakakin majalisar, Kabiru Rurum, wanda ya sanar da hakan a taron majalisar na ranar alhamis a Kano, yace majalisar ta samu sakon wasikun gidan gwamnatin jihar har guda biyu.

Kamar yanda yake a wasikar; Injiniya Bashir Yahaya Karaye, Mukhtar Ishak Yakasai, Shehu Na'Allah Kura da Muhammad Tahar wanda aka fi sani da Baba Impossible.

Kakakin ya karanto wasika ta biyu daga gwamnan ta hannun mataimakin shi na bukatar majalisar ta bashi damar zabar Amina Inuwa Sa'id a matsayin Odita janar ta jihar.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

"Mun kuma samu sakon wata wasika da take bukatar damar yin sabuwar kwalejin kiyon lafiya, kimiyya da fasaha," iniji kakakin.

Mista Rurum yayi kira ga wadanda aka kawo sunayen sun dasu bayyana a gaban majalisa a ranar laraba, 2 ga watan janairu don tantancewa da tabbatarwa.

A taron ranar ne majalisar ta samu rahoton kwamitin kiyasin kasafin kudin shekarar 2019.

Bayan muhawara mai zafi tsakanin mahukuntan, sai suka amince da rahoton tare da umartar kwamitin da yayi gyare gyare kafin ranar litinin mai zuwa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel