Da duminsa: Hukumar 'yan sanda tayi karin haske kan mamaye gida Dino Melaye

Da duminsa: Hukumar 'yan sanda tayi karin haske kan mamaye gida Dino Melaye

Hukumar 'yan sandan Najeriya tayi magana a kan mamaye gidan Sanata Dino Melaye da ke Maitama a Abuja da 'yan sanda su kayi.

Yan sandan sun bayyana a gidan Sanatan ne inda suka neman kama shi domin tafiya da shi ofishin su.

Wannan na faruwa ne kwanaki biyu bayan Sanatan ya sanar da cewa Sufeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris yana shirin kama shi domin a ayi amfani da guba a kashe shi.

A aka tuntube shi, mai magana da yawun 'yan sanda, DCP Jimoh Moshood ya ce ba zai iya tabbatarwa a yanzu ba idan 'yan sanda sun mamaye gidan Dino Melaye.

Sai dai, ya kuma ce jami'an 'yan sanda suna da ikon gudanar da aikinsu bisa doka a duk inda ya kama.

Da duminsa: Hukumar 'yan sanda tayi karin haske kan mamaye gida Dino Melaye

Da duminsa: Hukumar 'yan sanda tayi karin haske kan mamaye gida Dino Melaye
Source: UGC

DUBA WANNAN: Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

Moshood ya ce 'yan sandan suna iya zuwa gidan Sanatan idan suna zargin ana shirin aikata wani laifi ko kuma idan an shigar da kara a kan Sanatan.

Rahotani sun ce 'yan sandan sun iso gidan Dino Melaye misalin karfe 12.30 na rana cikin motocci kuma daga bisani sun samu damar shiga gidan Sanatan.

Yan sandan sunyi amfani da motocci guda biyu sun tare kofar fita daga gidan sanatan yayin da wasu jami'an yan sandan suka tsaya a waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel