KARIN BAYANI: Dino Melaye ya boye cikin gidansa, yan sanda sun shiga tsamoshi

KARIN BAYANI: Dino Melaye ya boye cikin gidansa, yan sanda sun shiga tsamoshi

Sanata mai wakiltan jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye, yayi lambo cikin gidansa ya ki fitowa yayinda jami'an yan sandan Najeriya akalla 30 suka dira gidansa.

A lokacin muka kawo wannan rahoton, Dino Melaye, na cikin gidan. Yayinda manema labarai suka isa unguwar da na'urorinsu domin ganin abinda ke faruwa, shugaban tawagar jami'an tsaro ya bukacesu su bayar wajen saboda basu son duniya ta san abinda ke faruwa.

Yayinda aka tambayesa kan dalilin da yasa suka kawo farmaki, hafsan yan sandan yace kawai an basu umurni ne kuma ba zai fadada magana kan haka ba.

A yanzu haka, yan sandan sun shiga tsamoshi daga cikin gidan.

KARIN BAYANI: Dino Melaye ya boye cikin gidansa, yan sanda sun shiga tsamoshi

KARIN BAYANI: Dino Melaye ya boye cikin gidansa, yan sanda sun shiga tsamoshi
Source: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa wata ayarin jami'an hukumar yan sanda sun kai farmaki gidan shahrarren dan majalisan nan Sanata Dino Melaye, mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan tarayya.

Yan sanda sun dira a gidansa dake 11 Sangha street, off Mississippi, Maitama, birnin tarayya Abuja misalin karfe 12 na rana.

A yayinda aka bada wannan rahoton, jami'an yan sanda sun mamaye titin gidan Melaye da motoci kirar Toyota Hilux.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel