Zaben 2019: Rundunar soji ta fara atisayen rawar Mesa a fadin Nigeria

Zaben 2019: Rundunar soji ta fara atisayen rawar Mesa a fadin Nigeria

- Rundunar sojin Nigeria ta sanar da fara atisayen Egwu Eke 111, wanda aka fi sani da atisayen rawar Mesa, a fadin jihohi 36 da ke tarayyar Nigeria

- Laftanal Janar Buratai ya ce rundunar sojin ta fara atisayen ne da nufin shirya magance matsalolin tsaro da ka iya tasowa a zabukan 2019 da ke gabatowa

- Buratai ya ce za a kwashe tsawon watanni biyu, daga 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Fabreru ana atisayen

A ranar Juma'a, rundunar sojin Nigeria ta sanar da fara atisayen Egwu Eke 111, wanda aka fi sani da atisayen rawar Mesa, a fadin jihohi 36 da ke tarayyar Nigeria, da nufin shirya magance matsalolin tsaro da ka iya tasowa a zabukan 2019 da ke gabatowa.

Hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Y Buratai, wanda ya bayyana hakan a bukin kaddamar da atisayen a Maiduguri, jihar Borno, ya ce za a kwashe tsawon watanni biyu, daga 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Fabreru ana atisayen, wanda zai dakile wasu matsaloli na tsaro da ka iya tasowa a tsakanin lokutan.

KARANTA WANNAN:

Zaben 2019: Rundunar soji ta fara atisayen rawar Mesa a fadin Nigeria

Zaben 2019: Rundunar soji ta fara atisayen rawar Mesa a fadin Nigeria
Source: Depositphotos

Buratai ya ce: "Atisayen ya zama wajibi ne don dakile duk wasu matsalolin tsaro da ka iya zama barazana a kasar musamman na ta'addanci, garkuwa da mutane, 'yan bindiga da kuma barayin shanu.

"Wadannan nau'o'in ta'addancin barazana ne da ka iya kawo matsala ga zabukan 2019, wanda ya sa dole muka gabatar da wannan atisaye a jihohi 36 da ke fadin tarayyar kasar."

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel