Ta tabbata baka da cikakken ilimi a fannin man fetur - Adesina ya caccaki Atiku

Ta tabbata baka da cikakken ilimi a fannin man fetur - Adesina ya caccaki Atiku

- Femi Adesina, ya ce Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ba shi da cikakken ilimi idan har aka zo fannin man fetur na kasar

- Adesina ya caccaki Atiku, sakamakon kalubalantar kasafin kudin kasar na 2019 da shugaban kasa Buhari ya gabatar

- Adesina ya ce Atiku bashi da wata mafita akan dukkanin wadannan matsaloli da ya ke kallo sun dabaibaye kasafin kudin da shugaban kasa Buhari ya gabatar

Femi Adesina, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ba shi da cikakken ilimi idan har aka zo fannin man fetur na kasar.

Adesina ya bayyana hakan ne a cikin wata makala, wacce a cikinta ya caccaki dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar PDP, sakamakon kalubalantar kasafin kudin kasar na 2019 da shugaban kasa Buhari ya gabatar.

Ya buga misalai da wasu batutuwa da Atiku ya yi tsokaci akansu, da suka hada da farashin danyen mai da kuma kudaden ajiyar kasar a kasashen waje, ci gaba da biyan kudade ga kamfanin NNPC da kuma tattara kayayyakin amfani da su na kasar.

KARANTA WANNAN: Ku gabatar da hujjoji na cewar Buhari mai cin hanci ne - Keyamo ya kalubalanci PDP

Ta tabbata baka da cikakken ilimi a fannin man fetur - Adesina ya caccaki Atiku

Ta tabbata baka da cikakken ilimi a fannin man fetur - Adesina ya caccaki Atiku
Source: Twitter

Adesina ya ce Atiku bashi da wata mafita akan dukkanin wadannan matsaloli da ya ke kallo sun dabaibaye kasafin kudin, wanda kuma hakan kawai yana yi ne don kalubalantar kokarin gwanatin shugaban kasa Buhari na kawo karshen matsalolin.

"Dukkanin matsalolin da Atiku Abubakar ya lissafa, bashi da mafita akansu, wanda kuma ya nuna cewa yana da karancin ilimi musamman a fannin man fetur na kasar. Kowa ya san cewa kasar na kokarin samun kudaden aiwatar da ayyukan kasafin kudin ta kowacce fuska, don haka jawabin Atiku akan kasafin kudin kamar rainin hankaline, da kuma nuna tsantsar adawarsa ga gwamnatin Buhari," a cewar Adesina.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel