YANZU-YANZU: Yan sanda sun kai farmaki gidan Dino Melaye

YANZU-YANZU: Yan sanda sun kai farmaki gidan Dino Melaye

Ayarin jami'an hukumar yan sanda sun kai farmaki gidan shahrarren dan majalisan nan Sanata Dino Melaye, mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan tarayya.

Yan sanda sun dira a gidansa dake 11 Sangha street, off Mississippi, Maitama, birnin tarayya Abuja misalin karfe 12 na rana.

A yayinda aka bada wannan rahoton, jami'an yan sanda sun mamaye titin gidan Melaye da motoci kirar Toyota Hilux.

YANZU-YANZU: Yan sanda sun kai farmaki gidan Dino Melaye

YANZU-YANZU: Yan sanda sun kai farmaki gidan Dino Melaye
Source: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa sanata Dino Melaye na jihar Kogi ya koka ga sufeto-janar na yan sanda, Ibrahim Idris, inda yayi ikirarin cewa ana shirya munakisan kama shi a ranar Kirsimeti sannan a kashe shi.

A wani rubutu da ya wallafa a ranar Talata, 25 ga watan Disamba, dan majalisan daga Kogi yayi ikirarin cewa ana shirin yi masa alluran mutuwa.

Yace: “Akwai wani shiri daga IGP na kama nu a yau sannan ayi mani allura mutuwa. Tuni an turo jami’ai. An tsige kwamishinan Kogi da wasu. Yan Najeriya ku zuba idanu."

Amma rundunar yan sandan Najeriya a ranar Laraba, 26 a watan Disamba ta karyata shirin kamawa da kashe Sanata Dino Melaye.

A wata sanarwa daga kakakin yan sanda, DCP Jimooh Moshood yace wani jawabi da Sanata Dino Melaye yayi na cewa “IG na shirn kama shi da yi masa alluranmutuwa,” karya ne.

Moshood yace: “Rundunar ta bayyana cewa jwain makirci ne da kuma haddasa fitina wanda ka iya ba jama’a dariya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel