Har yanzu mu kadai ke iya zabga manyan kayan aikin lantarki a dun yammacin Afirka

Har yanzu mu kadai ke iya zabga manyan kayan aikin lantarki a dun yammacin Afirka

- Najeriya ce kasar da take hada wayoyi masu daukar manyan injina a Afirka ta yamma

- Hakan yasa ta zama ta shida a Nahiyar Afirka

- Bankin masana'antu ne ke tallafa mana inij Onafowokan

Har yanzu mu kadai ke iya zabga manyan kayan aikin lantarki a dun yammacin Afirka

Har yanzu mu kadai ke iya zabga manyan kayan aikin lantarki a dun yammacin Afirka
Source: Facebook

A duk fadin Afirka ta yamma Najeriya ce kasar da take hada wayar lantarki mai daukar manyan injina sannan kuma kasa ta shida a Afirka da ta dau salon fasaha.

Manajan daraktan kamfanin hada wayoyin lantarki da wayoyi masu daukar manyan injina na Coleman, George Onafowokan, yace haka a wata tattaunawa a ranar laraba.

Ya dangantaka cigaban bangaren da abubuwa kamar: tsari mai kyau, maida hankali , jajircewa, horarwa, kwarewar ma'aikata da kuma tallafin Nigerian Content Development and Monitoring Board (NCDMB).

Onafowokan yace: "A halin yanzu Najeriya ce kasa daya tak a Afirka ta yamma dake hada wayoyin lantarki masu daukar manyan injina. Muna hada wayoyin dake daukar manyan injina hakan yasa muka zama na shida a Nahiyar."

Yace masana'antar ta habaka kuma zata cigaba da habaka saboda tsarin ta, kari da cewa: "Nasarorin nan da muka samu duk a kasa da shekaru 20 ne. Sirrin nasarar nan kuwa ita ce mu da kungiyar mu. Ni a matsayina na shugaban kungiyar, na yarda da burin Najeriya, na yarda cewa bazamu siyar da wayoyin lantarki da aka shigo dasu daga wasu kasashe ba."

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

"Gaskiya mun maida hankali, mutane da yawa da masana'antu na jinjina mana akan jajircewar mu. Muna maida hankali gurin horar da yan Najeriya, gani da cewa yan Najeriya na da fasahar da zasu yi abubuwan fasaha da mu bazamu iya ba. Horarwa ne da kuma jajircewa."

Onafowokan,wanda ya jinjinawa aiyukan NCDMB yace: "Muna samun tallafi daga bankin masana'antu. Hakan na taka rawar gani wurin cigaban mu. Da Babu BOI ,bazamu kai inda muke ba saboda idan ka dogara da bankunan yan kasuwa bazaka samu cigaba ba saboda suna saka riba mai yawa. A takaice ma ribar da suke sawa ta isa ta karya mutum."

"Ana amfani da wayoyin a bututun dake cikin ruwa da kuma masana'antu hako ma'adanai. Muna kuma fatan mu fara aiyuka masana'antun mai da iskar gas."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel