Yari ya kwace min hakkokina – Mataimakin gwamna

Yari ya kwace min hakkokina – Mataimakin gwamna

- Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala Muhammad, ya zargi gwamnatin jihar da kwace masa hakokinsa ta fannin kudi

- A cewarsa hakan ya faru ne tun bayan da ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar kujerar gwamna a jihar.

- Ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da addu’a domin samun zaman lafiya mai dorewa cewa karshen ne yafi muhimmanci ba farkon ba

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala Muhammad, yace gwamnatin jihar ta kwace masa hakokinsa ta fannin kudi tun bayan da ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar kujerar gwamna a jihar.

Yari ya kwace min hakkokina – Mataimakin gwamna

Yari ya kwace min hakkokina – Mataimakin gwamna
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Muhammad ya bayyana cewa shi bai yarda da cewa gwamnatin na abubuwa yadda ya kamata ba sannan saboda haka cewa ake hukunta shi a siyasance.

Ya bukaci mutanen jihar das u ci gaba da addu’a domin samun zaman lafiya mai dorewa cewa karshen ne yafi muhimmanci ba farkon ba.

KU KARANTA KUMA: Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah

A wani lamari na daban, mun ji cewa Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo karshen hare-haren da yan fashi ke kai wa jihar Zamfara idar har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Dan takarar shugaban kasar yace lokacin da aka yi zaben Ekiti da Osun, shugaba Buhari ya tura jami’an yan sanda da sojoji 30,000 don su kula da zaben.

Ya bayyana cewa yafi muhimmanci gare shi ya kare rayukan mutanen jihar fiye da kare mulkin siyasa na jam’iyyarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel