Ku gabatar da hujjoji na cewar Buhari mai cin hanci ne - Keyamo ya kalubalanci PDP

Ku gabatar da hujjoji na cewar Buhari mai cin hanci ne - Keyamo ya kalubalanci PDP

- Festus Keyamo (SAN), ya kalubalanci PDP da d'an takararta, Atiku Abubakar, da su gabatar da hujjoji akan zargin da sukewa Buhari na cewar yana cin hanci da rashawa

- A ranar Alhamis, Atiku Abubakar ya zargi iyalan shugaban kasar da mallakar kamfanin sadarwa na Etisalat Nigeria, da kuma bankin KeyStone

- Keyamo ya ce Atiku da PDP basa bukatar wani ya rinka damuwa da kalamansu, inda ya bukaci 'yan Nigeria da su matsa lamba kan lallai sai 'yan adawar sun gabatar da hujjoji

Mai magana da yawun kkungiyar yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Festus Keyamo (SAN), ya kalubalanci jam'iyyar PDP da d'an takararta, Atiku Abubakar, da su gabatar da hujjoji akan zargin da sukewa shugaba Buhari na cewar yana cin hanci da rashawa, idan har suna da su.

Ya ce ya zama wajibi 'yan Nigeria, musamman masu amfani da kafafen da zumunta na zamani su kasance masu neman hujjoji daga PDP kan wannan zargi da aka yiwa APC da shugaba Buhari, tunda dai sharri ne na cin hanci da rashawa.

Keyamo ya bayyana haka ne a matsayin martani ga Atiku Abubakar, wanda ta hannun mai tallafa masa ta fuskar watsa labarai, Mr Phrank Shaibu, ya zargi iyalan shugaban kasar da mallakar kamfanin sadarwa na Etisalat Nigeria, da hannun jari na akalla $2bn (N727bn akan canjin N360 kowacce dala 1).

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi warwas - Kasafin Buhari na 2019 na cikin hatsari

Ku gabatar da hujjoji na cewar Buhari mai cin hanci ne - Keyamo ya kalubalanci PDP

Ku gabatar da hujjoji na cewar Buhari mai cin hanci ne - Keyamo ya kalubalanci PDP
Source: Depositphotos

A yayin da yake kafa hujja da wani rahoto, Atiku ya kuma zargi iyalan Buhari da mallakar bankin Keystone, da hannun jari akalla $1.916bn (wanda yayi dai-dai da N307.5bn) da kuma mallakar akalla hannun jari na N3bn a sabon bankin Pakistani Islamic Bank.

Keyamo ya ce Atiku da PDP basa bukatar wani ya rinka damuwa da kalamansu, inda ya bukaci 'yan Nigeria da su matsa lamba kan lallai sai 'yan adawar sun gabatar da hujjoji na wadannan zarge zarge da suka yi akan shugaban kasar da iyalansa.

Haka zalika shima atiku yayi zargin cewa N1.7bn da manoman Nigeria suka shirya tarawa don tallafawa yakin zaben Buhari, ya saba da sashe na 91 (9) na kundin dokar zabe ta 2010 (kamar yadda aka sabunta), wanda ya ce, babu wani mutum daya ko gungun jama'a da zasu hada N1m ga d'an takara ko jam'iyya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel