Atiku yayi alkawarin kawo karshen kashe-kashen Zamfara idan aka zabe shi shugaban kasa a 2019

Atiku yayi alkawarin kawo karshen kashe-kashen Zamfara idan aka zabe shi shugaban kasa a 2019

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo karshen hare-haren da yan fashi ke kai wa jihar Zamfara idar har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Dan takarar shugaban kasar yace lokacin da aka yi zaben Ekiti da Osun, shugaba Buhari ya tura jami’an yan sanda da sojoji 30,000 don su kula da zaben.

Ya bayyana cewa yafi muhimmanci gare shi ya kare rayukan mutanen jihar fiye da kare mulkin siyasa na jam’iyyarsa.

Atiku ya kuma yi ta’a ziya ga mutanen Zamfara kan mawuyacin halin da suke ciki a hannun yan fashi da makami.

Kalli bidiyon a kasa:

Ministan harkokin cikin gida, Laftanat Janar Abdulrahman Dambazau (mai murabus) ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta karo jami'an tsaro zuwa jihar Zamfara domin ganin an kawo karshen kashe-kashen mutane da asarar dukiyoyi.

KU KARANTA KUMA: Za mu kawo wa Buhari kuri’u miliyan 20 – Miyetti Allah

Dambazau ya bayar da wannan tabbacin ne a wata sako da ta fito daga bakin mai magana da yawun sa, Osaigbovo Ehisienmen a ranar Alhamis a Abuja.

Ministan ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta'azziyarsa ga gwamnati da al'ummar jihar Zamfara bisa rasa rayyuka da dukiyoyi da akayi sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar cikin 'yan kwanakin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel