2019: Dalilin da ya sanya mu ke da tabbacin nasarar Buhari - Oshiomhole

2019: Dalilin da ya sanya mu ke da tabbacin nasarar Buhari - Oshiomhole

Za ku ji cewa, shugaban jam'iyyar APC mai mulki na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya na kan ganiyarsa ta ci gaba da kyautata zato gami da sa rai da kuma fatan nasarar jam'iyyarsa a kakar babban zaben kasa na shekarar badi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Kwamared Adams Oshiomhole, ya ce rana ba ta karya sai dai ko uwar diya ta ji kunya domin kuwa ba bu wata makawa nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 sai ta tabbata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa ta Villa jim kadan bayan ganawarsa ta sirrance da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a jiya Alhamis.

2019: Dalilin da ya sanya mu ke da tabbacin nasarar Buhari - Oshiomhole

2019: Dalilin da ya sanya mu ke da tabbacin nasarar Buhari - Oshiomhole
Source: Twitter

Yayin zayyana dalilan sa ga manema labarai, Oshiomhole ya ce a halin yanzu jam'iyyar adawa ta PDP ba ta kasance zabi ga 'yan Najeriya ba da ko shakka ba bu ba su da niyyar kada ma ta kuri'u a zaben badi.

Duk da yunkurin jam'iyyar PDP na mulkar kasar nan tsawon shekaru 60, 'yan Najeriya sun shata mata layi bayan shekaru 16 kacal da hakan yake nuni da kosawar su da ita kamar yadda Kwamared Oshiomhole ya labarta.

KARANTA KUMA: Matashin 'dan kasuwa ya yiwa 'Yar shekara 6 fyade a jihar Kano

Bugu da kari Oshiomhole ya bayyana cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba ya da wata cancanta ta jagorantar Najeriya duba da yadda ya kasance cikin jam'iyyar tsamo-tsamo tsawon shekaru 16 da ta nemi ta durkusar da kasar nan ba tare da an farga ba.

Shugaban jam'iyyar ya kuma yi furuci dangane da shirin jam'iyyarsa na kaddamar ya yakin neman zaben kujerar shugaban kasa a yau Juma'a cikin birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel