2019: Gwamna Amosun ya yi wa Buhari kamfen a Ogun

2019: Gwamna Amosun ya yi wa Buhari kamfen a Ogun

- Gwamna Ibikunle Amosun, ya fara kamfen dinsa a yankin Ogun ta tsakiya

- Ya yi alkawarin samar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da na tarayya domin ci gaba da kawo tarin ci gaba a yankin

- Amosun ya kuma yi amfani da damar wajen yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen din zagayensa na biyu wadda a cewarsa shine zai iya sauya Najeriya zuwa tafarkin ci gaba

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya fara kamfen dinsa a yankin Ogun ta tsakiya tare da alkawarin samar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da na tarayya domin ci gaba da kawo tarin ci gaba a yankin mazabar.

Taron wanda ya samu halartan mutane da yawa ciki wakilan kungiyoyin jama’a da dama wanan shine kamfen din farko da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar ta shirya tun bayan da rikici ya barke a cikinta kan tsarin zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka yi a watan Oktoba.

2019: Gwamna Amosun na yi wa Buhari kamfen a Ogun

2019: Gwamna Amosun na yi wa Buhari kamfen a Ogun
Source: Depositphotos

Sanata Amosun ya kuma yi amfani da damar wajen yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen din zagayensa na biyu wadda a cewarsa shine zai iya sauya Najeriya zuwa tafarkin ci gaba.

Yace shugaba Buhari ya fatattaki yaki da cin hanci da rashawa sannan ya mayar da hankali wajen yin ayyukan ci gaba wanda shine tushen kowani ci gaba na tattalin arziki.

KU KARANTA KUMA: A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu – Gwamnan APC

A wani lamari na daban, mun ji cewa akalla mambobin jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP) 50,000, ciki harda wani tsohon hadimin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Party (APC), a jihar Sokoto a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba.

Masu sauya shekar sun koma APC ne tare da tsohon shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Chika Umar Dantama, tsohon dan takarar dan majalisar dokokin jiha a jam’iyyar a 2015, da kuma jami’ai da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel