A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu – Gwamnan APC

A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu – Gwamnan APC

- Gwamnan jihar Nassarawa ya ce kamata yayi a bar kowace jiha ta tantance karancin albashi da za ta iya biyan ma'aikatanta

- Kungiyar kwadago dai ta fake kan cewa N30,000 take so a biya a matsayin mafi karancin albashi

- Almakura ya ce a lokacin da wasu jihohin za su iya biyan sama da 30,000 a matsayin karancin albashi ga ma'aikata, akwai jihohi wadanda a yanzu da kyar suke iya 18,000

Gwamnan jihar Nassarawa ya bayyana ra’ayinsa akan batun Karin albashi inda ya ce kamata yayi a bar kowace jiha ta tantance karancin albashi da za ta iya biyan ma'aikatanta.

An dai dauki tsawon lokaci ana kai ruwa rana batun kan albashi mafi karanci da gwamnatoci da kamfanoni za su biya ma'aikata a fadin kasar.

A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu – Gwamnan APC

A bar Jihohi su biya albashi gwargwadon karfinsu – Gwamnan APC
Source: Twitter

Bayan tattaunawa da kungiyar kwadago gwamnatin tarayya na ganin cewa N30,000 ne abinda ya dace a biya a matsayin karancin albashi.

Sai dai gwamnonin jihohi sun ce ba za su iya biyan hakan ba.

Gwamnan jihar Nassarawa, Umar Tanko Almakura ya ce a lokacin da wasu jihohin za su iya biyan sama da dubu 30 a matsayin karancin albashi ga ma'aikata, akwai jihohi wadanda a yanzu da kyar suke iya biyan Naira dubu 18, wato kimanin Dalar Amurka 50, wanda shi ne karancin albashin ma'aikata da ake amfani da shi a kasar.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Tambuwal da wasu sun sauya sheka zuwa APC a Sokoto

Gwamnan ya kuma ce za a samu matsala idan aka ce kananan jihohi su biya ma'aikata albashi daidai da na jihohi masu karfin tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel