Iyalin Marigayi Alex Badeh sun yi watsi da rahoton binciken ‘Yan Sanda

Iyalin Marigayi Alex Badeh sun yi watsi da rahoton binciken ‘Yan Sanda

Mun samu labari daga jaridar Vanguard cewa iyalin tsohon hafsun sojan Najeriya da aka kashe kwanaki, Air Vice Marshal, Alex Badeh, sun karyata ikirarin da Makasan su ka bada na dalilin kashe shi.

Iyalin Marigayi Alex Badeh sun yi watsi da rahoton binciken ‘Yan Sanda

Iyalin Marigayi Badeh sun karyata makasan sa sun ce ranar da aka kashe shi bai da kudi
Source: Twitter

Iyalan Air Vice Marshal, Alex Badeh sun bayyanawa ‘yan jarida cewa abin da wadanda aka kama da laifin kashe tsohon sojan su ka fada na cewa sun kashe shi ne domin su yi gaba da wasu makudan kudi da ke hannun sa, ba gaskiya bane.

Daya daga cikin dangin Marigayin yake cewa, ba su ji dadin abin da ake yadawa ba, na cewa Alex Badeh yana dauke da makudan kudi ne da yayi niyyar sayen wasu karin gonaki a lokacin da aka kashe sa. Iyalan baban Sojan sun karyata wannan.

KU KARANTA: Yadda mu ka kashe Alex Badeh inji daya daga cikin makasan Marigayin

‘Dan uwan na sa yace lokacin da aka yi wa Badeh kisan gilla, bai da N500 ko N1000 a hannun sa ko a cikin mota kamar yadda Makasan na sa su ka raya. Dangin Marigayin su kace har ta kai Marigayin ya sallami wasu ma’aikatan sa saboda rashin kudi.

Iyalin Marigayin sun ce asali ma an kashe Badeh ne yana kokarin zuwa gona domin ya saida hatsi, ya iya biyan ma’aikatan sa kudin aikin su. ‘Yan uwan sa sun ce ajali ya ritsa Badeh ne yana hanyar zuwa gonar sa ya saida buhunan masara ya samu kudi.

Wannan Bawan Allah yace kafin faruwar wannan abu, akwai wani Bakauye da ya zo wajen Marigayin yana neman taimakon kudin magani. Rashin kudi ya sa dole sai dai Alex Badeh ya auna masa masara, ya tafi ya saida a kasuwa ya samu kudi inji Iyalin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel