Ilmi zai canji arzikin man fetur idan na samu mulki inji Ezekwisili

Ilmi zai canji arzikin man fetur idan na samu mulki inji Ezekwisili

- Dr. Oby Ezekwesili ta shiga yawon kamfe a cikin Kudancin Najeriya

- ‘Yar takarar tace ta fi duk masu neman mulkin kasar nan cancanta

Ilmi zai canji arzikin man fetur idan na samu mulki inji Ezekwisili
Jirgin yakin Dr. Oby Ezekwesili ya isa Yankin Kudu maso Gabas
Asali: UGC

Tsohuwar Ministar Najeriya kuma ‘Yar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta Allied Congress Party of Nigeria, Dr. Oby Ezekwesili, gana da mutane domin fadakar da su game da manufar ta idan ta samu mulki.

Dr. Oby Ezekwesili ta gana da mutane a kan titi a Jihar Anambra inda ta rika bayyanawa jama’a abin da za tayi idan ta dare kan mulkin Najeriya a 2019. Ezekwesili tace ta fi duk sauran ‘Yan takaran shugaban kasar cancanta.

KU KARANTA: Gwamnan APC ya nemi mutane su ba Buhari goyon baya ya zarce

Ezekwesili da mutanen ta sun shiga har cikin jama’a ne a Garin Onitsha da ke yankin kudu maso gabas domin kamfen din da ta kira “Walko of Women”. ‘Yar takarar ta ACPN tace idan ta lashe zaben 2019, za ta gyara Najeriya.

Oby Ezekwesili wanda ta rike ministan ma’adanai da kuma ilmi a gwamnatin PDP, ta bayyana cewa idan har ta zama shugabar kasa, harkar ilmi ne zai zama abin da ke kawowa Najeriya tarin kudi a maimakon danyen man fetur.

Fitattan ‘Yar takarar ta cigaba da yin kiran da ta saba ga jama’a na su yi watsi da jam’iyyun PDP da APC wanda su kayi kaurin-suna a Najeriya, su mara mata baya a zaben 2019 domin kai kasar nan ga ci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel