Ba za mu yarda a karawa IGP wa’adi a 2019 ba - Inji Kungiyar CUPP

Ba za mu yarda a karawa IGP wa’adi a 2019 ba - Inji Kungiyar CUPP

Mun ji labari cewa kungiyar CUPP wanda hadaka ce ta jam’iyyun hamayya a Najeriya ta shigar da karar shugaba kasa Muhammadu Buhari a gaban kotu a dalilin yunkurin karawa shugaban ‘yan sanda wa’adi.

Ba za mu yarda a karawa IGP wa’adi bayan 2019 ba - CUPP

‘Yan adawa sun kai karar Shugaban kasa Buhari gaban Alkali
Source: Depositphotos

Kungiyar CUPP za ta kara da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban shari’a ne a game da shirin da aka bankado da gwamnatin tarayya ke yi na karawa Sufetan ‘Yan sandan Najeriya watau Ibrahim K. Idris wa’adin watanni 6.

Mai magana da yawun CUPP, Ikenga Ugochinyere, ya fadawa ‘yan jarida cewa sun maka gwamnatin Buhari a kotu ne domin tabbatar da cewa ba ayi wa dokar tsarin mulkin kasa karon-tsaye ba a kan wa’adin shugaban 'Yan Sanda.

KU KARANTA: Makiyayan Najeriya sun fitar da ‘Dan takarar 2019 tsakanin Atiku da Buhari

Yanzu dai kungiyar ta shigar da shugaba Buhari kara a gaban babban kotun tarayyar Najeriya da ke zama a Abuja. Sauran wadanda aka hada a cikin karar sun hada da shi karan kan-sa Sufeta na ‘Yan sandan kasar, Ibrahim K. Idris.

Haka-zalika kungiyar ta jam’iyyun adawan su na karar hukumar da ke kula da harkokin ‘Yan sanda watau PSC da kuma gidan ‘Yan sandan kasar kamar yadda Ugochinyere ya fadawa manema labarai a Garin Owerri da ke Jihar Imo.

A Junairun 2019 ne Sufetan ‘Yan sandan kasar zai cika shekara 60 a Duniya, a ka’ida ya kamata a ce an yi wa babban Jami’in ‘Yan sandan ritaya kafin wannan lokaci. CUPP tace kin nada sabon IG ya sabawa doka kuma ba su yarda ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel