2019: Yanzu ne lokacin da aka fi bukatar Buhari a Najeriya – Gwamnan Katsina

2019: Yanzu ne lokacin da aka fi bukatar Buhari a Najeriya – Gwamnan Katsina

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa akwai matukar bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce a kan mulki a 2019 domin ya gyara Najeriya.

2019: Yanzu ne lokacin da aka fi bukatar Buhari a Najeriya – Gwamnan Katsina

Masari yace Shugaba Buhari ya kamo hanyar gyara Najeriya
Source: Twitter

Aminu Bello Masari yayi kira ga jama’a su kara dafawa shugaban kasa Buhari wajen ganin ya zarce a kan mulki. Gwamna Masari yake cewa idan har Buhari bai koma kan karagar mulki, an yi asarar gyaran da aka soma

Rt. Hon Aminu Masari na Jihar Katsina yace gwamnatin Buhari tayi kokari ainun wajen daura Najeriya kan turba. Gwamnan yace yanzu an kamo hanyar gyara kwarai da gaske a shekaru 4 da APC tayi tana mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo da Oshiomhole sun yi ganawar sirri a Villa

Gwamnan ya bayyana cewa ne a lokacin da ya kaddamar da wasu ayyuka a Jihar, inda ya kawo hankalin jama’a cewa shugaban kasa Buhari mutum bane mai kokarin tara dukiya don haka ya kamata a kara zaben sa a 2019.

Aminu Masari yake cewa babu wanda ya cancanta ya mulki kasar nan a halin yanzu irin shugaba Muhammadu Buhari inda yace idan ba haka ba, an yi matukar wahalar banza a tafiyar da aka soma na gyara Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel