Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi warwas - Kasafin Buhari na 2019 na cikin hatsari

Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi warwas - Kasafin Buhari na 2019 na cikin hatsari

- A ranar Alhamis, 27 ga watan Disambar 2018, farashin danyen mai ya sauka daga $50 zuwa $48 a kasuwar mai ta duniya

- Hakan kuma ya kara tabbatar da cewa hasashen gwamnatin, musamman na gudanar da sabbin ayyuka da ke kunshe a cikin kasafin na 2019 ba zai tabbata ba

- Wannan kuma ya zo ne a lokacin da ake hasashen cewa danyen man Nigeria mai sinadarin Egina zai shiga kasuwar duniya a watan Fabreru, 2019

A ranar Alhamis, farashin danyen mai ya sauka daga $50 zuwa $48 a kasuwar mai ta duniya, wanda kuma hakan ke nuni da saukarsa kasa da $12 kamar yadda kasafin da shugaba Buhari ya gabatar, wanda yayi hasashen danyen man zai kai $60 don samun kudaden cimma ayyukan cikin kasafin.

Hakan kuma ya kara tabbatar da cewa hasashen gwamnatin, musamman ma na tattara dukkanin kudaden haraji da kuma gudanar da sabbin ayyuka da ke kunshe a cikin kasafin na 2019 ba zai tabbata ba.

Wannan kuma ya zo ne a lokacin da ake hasashen cewa danyen man Nigeria mai sinadarin Egina zai shiga kasuwar duniya a watan Fabreru, 2019, a cewar wani rahoto, wanda ya bayyana cewa babban jirgin ruwa da zai dauki sahun farko na safarar man Egina zai fara ne da kamfanonin Total, NNPC da kuma wani kamfani na kasar Sin mai suna CNOOC.

KARANTA WANNAN: Zanje kurkuku idan kuka sanar da 'yan Nigeria laifin dana aikata - Atiku ga Buhari, APC

Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi warwas - Kasafin Buhari na 2019 na cikin hatsari

Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi warwas - Kasafin Buhari na 2019 na cikin hatsari
Source: Depositphotos

Mai magana da yawun kamfanin Total, a ranar Alhamis, ya sanar da jaridar Vanguard a wayar tarho, cewar suna kan kokari na ganin cewa sahun farko na danyen man Egina daga wajensu ya shiga kasuwar duniya kafin karshen watan Disamba, 2018.

Kafin hakan, kamfanin ya bayyana cewa danyen man Egina na da matukar amfani, musamman yadda zai taimaka wajen kara ganga 200,000 a kowacce rana, daga wadanda suka saba hakowa.

Idan za a iya tunawa, a cikin kasafin 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar, shugaban kasar ya ce a matsayin gwamnatinsa mai cike da bin diddigi, zasu ci gaba da yin nazari kan lamarin, kuma zasu gaggauta daukar mataki da zaran an samu wasu canje canje na sauyawar farashin danyen man a kasuwar duniya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel