Kasafin kudi: Fashola zai kashe kusan Naira Biliyan 500 a 2019

Kasafin kudi: Fashola zai kashe kusan Naira Biliyan 500 a 2019

Ma’aikatar wutar lantarki da kuma gidaje da ayyukan Najeriya, ta yi kasafin Naira Biliyan 441.559 a matsayin abin da za ta kashe a shekara mai zuwa. Jaridar nan ta Daily Trust ce ta rahoto mana wannan labari.

Kasafin kudi: Fashola zai kashe kusan Naira Biliyan 500 a 2019

Kasafin kudi: Fashola zai kashe kusan Naira Biliyan 500 a 2019
Source: Depositphotos

Babatunde Fashola, yana sa ran kashe sama da Biliyan 440 a shekarar badi, inda yake so kusan Naira Biliyan 408 su shiga cikin kudin da aka ware domin gina abubuwan more rayuka da kuma sauran ayyuka na cigaban kasa.

A wancan makon ne shugaban kasa ya mikawa majalisar tarayya kundin kasafin kudin 2019, inda aka ga cewa gwamnatin kasar tayi kasafin Naira Tiriliyan 8.826. Minista Fashola zai samu kusan kashi 5% daga wannan kudin.

KU KARANTA: Najeriya ta kama hanyar shiga cikin sahun kasashe 14 da su ka fi karfin tattali

Babban Babatunde Fashola, zai kashe Biliyan 33.53 wajen biyan albashi da alawus da sauran hidima da hada-hadar ma’aikatar sa ne a shekara mai zuwa. Fiye da Biliyan 400 kuwa za su tafi ne wajen gina tituna da gadoji a kasar.

Akwai hukumomin ma’aikatar da za su samu makudan biliyoyi, daga ciki akwai FERMA mai gyaran hanyoyi da kuma hukumar da ke sa wuta a kauyuka watau REA. Haka kuma ba a bar hukumar TCN na lantarki a baya ba.

A kasafin da shugaba Muhammadu Buhariya gabatar, za a kashe Biliyan 4.3 wajen aikun wutan Zungeru da ke Jihar Neja. Sannan kuma za a kashe wasu makudan kudin domin gyara wutan lantarki a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel