Fusataccen gwamnan APC ya bayyana dalilin canjin shekar magoya bayansa

Fusataccen gwamnan APC ya bayyana dalilin canjin shekar magoya bayansa

A yau, Alhamis, ne gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun, ya ce magoya bayansa da hadimansa sun canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar APM saboda bacin rai.

Gwamnan ya yi wannan kalami ne yayin amsa tambayoyi daga 'yan jaridu a wurinn kaddamar da yakin neman zabensa a matsayinsa sanata da aka yi a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Amosun ya kaddamar da yakin neman zabensa ne daga fadar babban sarkin kasar Egba, Oba Adedotun Aremu Gbadebo.

Sarkin ya ce APC zata cinye dukkan zaben jihar ba tare da fuskantar wata tagangarda ba.

A cewar gwamna Amosun, 'yan jam'iyyar APM din sun fita daga APC ne bayan shugaban jam'iyyar ya fusatata su.

Fusataccen gwamnan APC ya bayyana dalilin canjin shekar magoya bayansa

Amosun
Source: Depositphotos

A jihar Ogun, Adekunle Akinlade, dan takarar gwamna Amosun, ya tattara wasu mambobin majalisar jihar tare da kwamishinoni zuwa jam'iyyar APM.

Bayan fitar Adekunle da sauran manyan gwamnatin ta Osun, gwamnan jihar, Amosun, ya fito ya bayyanawa cewar ya albarkaci matakin da suka dauka.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun daga ranar bajakolin wadanda suka kashe Alex Badeh

Duk da daurin gindin gwamna da yake da shi, Akinlade ya sha kasa a hannun attajirin dan kasuwar man fetur, Dapo Abiodun, a zaben fidda 'yan takara na jam'iyyar APC.

Akinlade ya ce ya canja sheka zuwa jam'iyyar APM tare da 'yan majalisar dokokin jihar Ogun 26 a yau, Litinin.

Fusatattun mambobin jam'iyyar ta APC a jihar Ogun sun bayyana, ta bakin kakakinsu, Lamidi Olatunji, cewar sun canja sheka zuwa jam'iyyar APM ne domin cika burinsu na yin takara bayan an yi ma su fashin tikitin takara a APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel