Mutane 2 kacal da ba su cin rashawa a Najeriya - inji Balarabe Musa

Mutane 2 kacal da ba su cin rashawa a Najeriya - inji Balarabe Musa

Daya daga cikin dattijan Arewa kuma tsohon dan gwagwarmaya dake zaman jagoran daya daga cikin jam'iyyun adawa watau Peoples Redemption Party (PRP) mai suna Balarabe Musa ya bayyana cewa kalar rukunin mutane biyu ne kacal ba sa tu'ammali da cin hanci da rashawa.

Fitaccen dan gwagwarmayar ya bayyana cewa yanayin turbar da kasar ta Najeriya ke kai gaba daya gurbatacce ne don haka ne ma kusan komai baya tafiya yadda ya kamata kuma cin hanci da rashawa yayiwa kasar katutu.

Mutane 2 kacal da ba su cin rashawa a Najeriya - inji Balarabe Musa

Mutane 2 kacal da ba su cin rashawa a Najeriya - inji Balarabe Musa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kwace gari sukutum a Borno

Legit.ng Hausa ta tsinkayi dan Gwagwarmayar Balarabe Musa da yake lissafa rukunin mutanen da cewa wadanda kawai ba da damar karbar rashawar ne da kuma wasu kalilan da basu kai kaso digo daya (0.1)a cikin dari ba ne kawai basa cin hanci a kasar.

A wani labarin kuma, Wata sabuwar kungiyar tsagerun Neja Delta dake ikirarin rajin kare hakkoki da kuma muradun yankin mai arzikin man fetur mai suna War Against Niger Delta Exploitation a turance sun ayyana barazanar kawo kancal ga zabukan 2019 masu zuwa.

Kungiyar dai ta bayyana cewa a shirye take ta hargitsa dukkan shirin gwamnatin tarayya na yin zabe a yankunan su idan dai har ba'a zauna an tattauna da su ba tare da magance masu matsalolin su da suka ce sun addabe su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel