2019: INEC ta kaddamar da manhajar wayar hannu domin magance magudin zabe

2019: INEC ta kaddamar da manhajar wayar hannu domin magance magudin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a kaddamar da wata manhaja ta musamman domin magance matsalar magudi a zabukan shekarar 2019.

Manhajar zata bawa 'yan Najeriya damar bayar da rahoton abinda ke faruwa a akwatunsu na zabe.

Sabuwar manhajar, da za a iya sakko da ita a wayar hannu daga shafin yanar gizo na INEC ko shafin sauke manhajoji na Google, zata iya bawa jami'an hukumar damar gano duk mazabar da aka sanar da samun wata matsala domin su gaggauta sanar da jami'an tsaron da zasu dauki matakin gaggawa.

2019: INEC ta kaddamar da manhajar wayar hannu domin magance magudin zabe

Ma'aikatan INEC
Source: Depositphotos

Dakta Mustapha Leeky, kwamishinan a hukumar zabe, ya bayyana cewar INEC ta bullo da manhajar ne domin dakile matsalar sayen kuri'u da aka fuskanta a zabukan jihohin Ekiti da Osun.

DUBA WANNAN: Duk 'yan uwan Buhari talakawa yanzu sun biloniyas - Buba Galadima

Ya ce, "mun kirkiri wata manhaja da bamu ji kafafen yada labarai na magana a kanta ba, a yanzu haka manhajar mai taken INEC i-reporter na nan a shafinmu na yanar gizo ko shafin sauke manhajoji na Google.

"Manhajar zata bawa 'yan Najeriya damar sanar da mu abinda ke faruwa a mazabunsu daga wayoyinsu na hannu ta hanyar aiko mana da hotuna kai tsaye. Mu kuma da mun samu sako zamu gano wacce mazaba ce kuma zamu dauki matakin da ya dace.

Kwamishinan ya kara da cewar sauke manhajar da amfani da ita kyauta ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel