An kama 'yan sanda hudu bisa zargin aikata fashi da makami

An kama 'yan sanda hudu bisa zargin aikata fashi da makami

- An damke wasu jami'an 'yan sanda 4 da ake zargi da yiwa wani dan kasuwa fashi da makami

- Dan kasuwan ya ce sunyi masa dukkan tsiya har da yi masa tsirara suka dauki hotunansa kafin kwace masa kudi

- Hukumar 'yan sanda ta kama 'yan sandan hudu tana bincikarsu kuma za a kore su daga aiki idan an tabbatar da zargin

An kama wasu jami'an 'yan sanda hudu da ke aiki da ofishin 'yan sanda na Ijanikan a Badagary na jihar Legas saboda fashin kudi da suka yiwa wani dan kasuwa dan Najeriya mazaunin kasar Togo inda suka kwace masa CFA 350,000.

A halin yanzu ana tsare da Sufeta Victor Amiete, Saja Samuel Gbemumu da Afolabi Oluwaseun da kofir Adigun Omotayo a hedkwatan 'yan sanda da ke Ikeja.

An gano cewa sun yiwa Theodore Ifunnaya fashi ne a ranar 17 ga watan Disambar 2018 a kusa da Iyana-Era a yayin da suke bincike a hanyar.

An samu 'yan sanda 4 da hannu dumu-dumu cikin fashi da makami

An samu 'yan sanda 4 da hannu dumu-dumu cikin fashi da makami
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

Ifunnaya dai ya dawo Najeriya ne domin ya yi bikin kirsimeti amma 'yan sandan suka kai shi zuwa caji ofis bayan sun lura akwai kudi a tare da shi. An gano cewar sun gana masa azaba sannan suka cire masa kaya suka dauki hotonsa kafin suka kwace kudaden na kasar waje.

Wadanda ake zargin sun gayyaci wani mai canjin kudi ya canja musu kudin kuma daga baya suka bashi N2,000 domin ya yi kudin mota zuwa Legas kuma su kayi barazanar cewa za su fitar da hotunnan a kafafen sada zumunta suyi masa sharri cewar an kama shi ne da fashi da makami da shiga kungiyar asiri.

Sai dai sunyi rashin sa'a 'yan uwan Ifunnaya sun san wata mataimakiyar kwamshinan 'yan sanda mai suna Hope Okafor ita kuma ta shigar da kara wajen DPO ta bukaci a kama su.

A yayin da ya ke tabbatar da kama su, mai magana da yawun 'yan sandan Legas, Chike Oti ya sake jadada cewa kwamishinan 'yan sandan baya ragawa wadanda aka samu da rashawa amma ya karyata cewa an yiwa mutumin tsirara a yayin da aka tsare shi.

Ya ce ana gudanar da bincike a kan zargin kuma idan ya tabbata suna da laifi za a kore su daga aikin dan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel