'Yan sanda sun daga ranar bajakolin wadanda suka kashe Alex Badeh

'Yan sanda sun daga ranar bajakolin wadanda suka kashe Alex Badeh

A yau, Alhamis, rundunar 'yan sanda ta kasa ta bayyana cewar ta daga bajakolin wadanda suka kashe tsohon shugaban rundunar askarawan soji ta kasa, Alex Badeh, ga manema labarai.

A jiya Laraba ne, rundunar 'yan sanda ta bayyana cewar tayi nasarar kama wadanda kashe Badeh yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga gonar sa dake garin Keffi, jihar Nasarawa, a ranar 18 ga watan Disamba.

Da yake bayyana nasarar kama wadanda ake zargin, DCP Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya ce an kama mutane 5 dake da hannu a kisan Badeh.

Moshood ya kara da cewa, rundunar 'yan sanda ta fasa gabatar da masu laifin ne saboda gudun kar ragowar dake da hannu a aikata laifin kisan su tsere.

'Yan sanda sun daga ranar bajakolin wadanda suka kashe Alex Badeh

Alex Badeh
Source: Twitter

"Yana da matukar muhimmanci mu sanar da cewar ba zamu samu damar gabatar da mutum biyu da wasu uku da ake zargi da hannu a kisan Badeh ba," a cewar Moshood.

Duk da ya ki ambaton sunansu, Moshood ya bayyana cewar biyu daga cikinsu na da alakar kai tsaye da kisan Badeh.

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kone makarantun Boko uku a Yobe

"Biyu daga cikin mutane 5 da muka kama na da hannu dumu-dumu a kisan Badeh, tsohon shugaban rundunar sojin sama ta kasa," a cewar Moshood.

Ya bayyana cewar mutanen biyar na tsare a magarkamar rundunar 'yan sanda, inda ake cigaba da kara bincike.

Kazalika ya bayyana cewar za a gabatar da dukkan masu hannu cikin kisan na Badeh ga manema labarai da jama'ar kasa da zarar rundunar 'yan sanda ta kamma bincikenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel