Kamfen: Buhari ya bawa Sanata Akpabio babban mukami

Kamfen: Buhari ya bawa Sanata Akpabio babban mukami

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban kwamitin goyon baya na shugaban kasa

- Yan asalin jihar Akwa Ibom hudu aka ba mukami a kwamtin shugaban kasar

- Shugaban kwamitin na jihar Okon ya bukaci mutanen jihar da su marawa Buhari baya don ganin yayi nasara a 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban kwamitin goyon baya na shugaban kasa gabannin zaben 2019.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kwamitin na jihar Akwa Ibom, Fasto Mfon Okon, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba a Uyo yace , yan asalin jihar hudu aka ba mukami a kwamtin.

Kamfen: Buhari ya bawa Sanata Akpabio babban mukami

Kamfen: Buhari ya bawa Sanata Akpabio babban mukami
Source: Depositphotos

Ya ce wadanda aka nada sun hada da Lady Valerie Ebe, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar a matsayin shugaba, kwamitin shawara na kasa, Sanata John Akpanudoedehe, daraktan tsare-tsare, Sanata Aloysius Etok, daraktan harkokin jam’iyyu daban-daban, da kuma jigon matan jam’iyyar na yankin kudu-maso-kudu, Rachael Akpabio, a matsayin mataimakiyar sakatariya.

KU KARANTA KUMA: Babu gurbi a fadar Villa har sai 2023: Marwa ga Atiku da sauransu

Okon yace nade-naden duk nuni ga cewa shugaba Buhari ya amince da kokarinsu na ganin yayi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Ya yi kira ga mutanen jihar da su fito a dama da su a siyasar kasar ta hanyar marawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) baya don ganin shugaban kasar ya kawo jihar Akwa Ibom a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel