Matashin 'dan kasuwa ya yiwa 'Yar shekara 6 fyade a jihar Kano

Matashin 'dan kasuwa ya yiwa 'Yar shekara 6 fyade a jihar Kano

Da yake dai Hausawa na cewa tsautsayi ba ya wuce ranar sa ko da kuwa ya auku ne bisa sanadi na ganganci, hakan ta ke kuwa domin mun rahoton cewa wani Matashin dan kasuwa ya debo ruwan dafa kansa a birnin Kanon Dabo da ke Arewacin Najeriya.

Za ku ji cewa wani matashin dan kasuwa, Saleh Musa mai shekaru 22 a duniya, a yau Alhamis ya gurfana gaban wata Kotun Majistire da ke zaman garin Kano bisa zargin sa da zakkewa wata kamar yarinyar da shekarunta na haihuwa ba su haura shida ba.

Kamar yadda majiyar rahoton ta zayyana, Saleh, wanda mazauni unguwar sheka ne da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, ya gurfana gaban kuliya da mummunan laifi na fyade bisa ma'auna ta kowace shari'a.

Matashin 'dan kasuwa ya yiwa 'Yar shekara 6 fyade a jihar Kano

Matashin 'dan kasuwa ya yiwa 'Yar shekara 6 fyade a jihar Kano
Source: UGC

Sufeto Pogu Lale, jami'in dan sanda mai shigar da kara gaban kotun ya bayar da shaidar cewa, wani Mutum Ya'u Muhammad, ke da alhakin shigar da korafin wannan mummunan lamari a ofishin 'yan sanda na unguwar Sheka tun a ranar 4 ga watan Dasumba na 2018.

Lale ya bayyanawa kotun cewa, Saleh ya aikata mummunar ta'ada ta zakkewa karamar yarinyar ne daura da wata Makarantar Firamare da ke unguwar Sheka da misalin karfe goma sha biyu na tsakar wannan rana.

Hakika wannan muguwar ta'ada ta sabawa sashe na 283 cikin kundin tsari na dokokin kasa kamar yadda Sufeto Lale ya bayyana.

KARANTA KUMA: Buhari, Osinbajo da Oshiomhole sun yi ganawar sirri a garin Abuja

Sai dai da ya ke hukunci na hannun Alkalin Kotun, Mai shari'a Muhammad Jibril, ya bayar da umarnin garkame Saleh a gidan kaso har zuwa ranar 10 ga watan Janairu na sabuwar shekara domin ci gaba da sauraron kararsa tare da zartar da hukunci daidai da abinda ya aikata.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani Matashi, Badamasi Abdullahi, ya amsa laifin sa na burkumawa kanwarsa juna biyu, Bara'atu Abdullahi a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel