Buhari, Osinbajo da Oshiomhole sun yi ganawar sirri a garin Abuja

Buhari, Osinbajo da Oshiomhole sun yi ganawar sirri a garin Abuja

Mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, sun shiga bayan Labule a fadar Villa da ke garin Abuja.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, ba bu wani sanannen rahoto dangane da ababen da jiga-jigan jam'iyyar suka tattauna yayin da suka kebance a fadar shugaban kasa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Buhari, Osinbajo da Oshiomhole sun yi ganawar sirri a garin Abuja

Buhari, Osinbajo da Oshiomhole sun yi ganawar sirri a garin Abuja
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, ana kyautata zaton kusoshin gwamnatin kasar sun tattauna ne dangane da yakin neman zaben jam'iyyar APC da za a kaddamar cikin birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma'a ta gobe.

Tuni dai shugaban kasa Buhari ya yi subul da baka cewa, jam'iyyar APC za ta kaddamar da yakin neman zaben ta nan ba da jimawa ba yayin da babban zaben kasa ya karato.

KARANTA KUMA: Kungiyar yakin neman zaben Atiku ta sha alwashin samun kuri'u 6m a zaben 2019

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, jam'iyyar sa ta APC za ta kaddamar da yakin neman zabe gadan-gadan a fadin kasar domin neman goyo bayan al'umma da ko shakka ba bu yake fatan hakan zai yi tasiri wajen cimma nasarar sa a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu na 2019.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, shugaba Buhari ya nada Sanata Akpabio a matsayin jagoran kwamitin goyon bayan yakin neman zaben sa, wanda ya kasance tsohon shugaba maras rinjaye a majalisar dattawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel