Buhari yayi ba’a ga Saraki, yace zai raba Kwara da dukkanin masu laifi kafin 2019

Buhari yayi ba’a ga Saraki, yace zai raba Kwara da dukkanin masu laifi kafin 2019

- Shugaba Buhari ya bayyana jajircewarsa na raba jihar Kwara da dukkanin masu laifi

- Buhari yace abun bakin ciki ne yadda jihar Kwara ta shiga labarai marasa dadin ji a yan baya-baya nan

- Ya fadi hakan yayin kaddamar da sansanonin yan sanda da garin Offa da ke jihar Kwara

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jajircewarsa na raba jihar Kwara da dukkanin masu laifi gabannin zaben 2019 me zuwa sakamakon duba da yayi ga rashin ci gaba da jihar ke fama da shi a baya-bayan nan.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba a karamar hukumar Offa da ke jihar, yayin kaddamar da sansanonin yan sanda da garin ta gina wanda kudinsa ya kai naira miliya 700 ta kuma bayar da shi a matsayin gudunmawa ga rundunar yan sandan Najeriya.

Buhari yayi ba’a ga Saraki, yace zai raba Kwara da dukkanin masu laifi kafin 2019

Buhari yayi ba’a ga Saraki, yace zai raba Kwara da dukkanin masu laifi kafin 2019
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris ya amince da aiki, domin bunkasa tsaro a ciki da kewayen garin biyo bayan kisan mutane talatin da uku da wasu yan fashi suka yi a ranar 5 ga watan Afrilu a harin da aka kai wasu bankunan Offa, lamarin da ya haifar da jimami a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Babu gurbi a fadar Villa har sai 2023: Marwa ga Atiku da sauransu

Da ya samu wakilcin ministan labarai da al’’adu, Alhaji Lai Mohammed a wajen taron, Buhari yace abun bakin ciki ne yadda jihar Kwara ta shiga labarai marasa dadin ji a yan baya-baya nan.

Ya kuma bukaci hukumomin tsaro da na yan sanda da su tabbatar da sun tsaurara matakan tsaro da kuma binciko masu laifi a fadin jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel