Zanje kurkuku idan kuka sanar da 'yan Nigeria laifin dana aikata - Atiku ga Buhari, APC

Zanje kurkuku idan kuka sanar da 'yan Nigeria laifin dana aikata - Atiku ga Buhari, APC

- Atiku Abubakar, ya kalubalanci jam'iyyar APC da shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari da su sanar da 'yan Nigeria laifukan da ya aikata kafin turashi kurkuku

- Ko a ranar Laraba, Atiku ya caccaki Buhari da cewar tafiyar hawainiya da gwamnatinsa ke yi ce silar gaza magance matsalar cin hanci da rashawa

- Sai dai kungiyar yakin zaben Buhari (PMBCO) ta caccake shi akan Buhari, wanda ta ce ya aikata laifukan da ya kamata ace yana kurkuku yanzu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kalubalanci jam'iyyar APC da shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari da su sanar da 'yan Nigeria laifukan da ya aikata kafin turashi kurkuku.

Atiku wanda ya mayar da wannan martanin ne bayan da kungiyar yakin zaben Buhari (PMBCO) ta caccake shi akan Buhari, wanda ya zargi tafiyar hawainiya da gwamnatin ke yi a matsain silar gaza magance matsalar cin hanci da rashawa.

Atiku wanda ya yiwa Buhari wankin babban bargo a ranar Laraba, ta hanyar cewa, "Buhari, tafiyar hawainiyarka bata da wata alaka da tsarin gudanarwar Nigeria. Kai kanka kasan ka gaza, ka daina neman tudun dafawa saboda 'yan Nigeria sun riga da sun gano cewa karya ce kayi masu tsagoranta."

KARANTA WANNAN: Na kama kwarto turmi da tabarya da matata - Magidanci ya sanar da kotu

Zanje kurkuku idan kuka sanar da 'yan Nigeria laifin dana aikata - Atiku ga Buhari, APC

Zanje kurkuku idan kuka sanar da 'yan Nigeria laifin dana aikata - Atiku ga Buhari, APC
Source: Depositphotos

Dan takarar shugaban kasar karkashin PDP ya ce: "Sam bana tsoron zuwa kurkuku, amma gwamnatin APC ta fara bayyanawa 'yan Nigeria shaidu na laifukan da suke zargin na aikata, ni kuma zan yarda a kamani, a kaini kurkuku.

"Har kullum Inuwa ce zata ci gaba da kasancewa baiwa ga haske, Nigeria na da 'yancin samun rayuwa mai alfanu, ba wai ta hayar yin karya ba, ba sai 'yan Nigeria sun mace kafin gwamnatin APC ta farka ba."

Atiku ya ce idan har mutum ya ci amanar mutane, sai ya fara borin kunya ta hanyar dora laifin ga wanda ke kusa da shi, "to kamar hakane APC take yi, suna tsoron sauka daga mulki, cikin jin kunyar gazawar da suka yi."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel