Kungiyar yakin neman zaben Atiku ta sha alwashin samun kuri'u 6m a zaben 2019

Kungiyar yakin neman zaben Atiku ta sha alwashin samun kuri'u 6m a zaben 2019

Lallai ko shakka ba bu kowane tsuntsu kukan gidansu yake domin kuwa a halin yanzu jaridar Legit.ng ta samu rahoton cewa, kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa ga dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ta sha alwashin yi masa sha tara ta arziki a zaben 2019.

Majiyar rahoton da ta tatso rahoton ta bayyana cewa, kungiyar nan ta The Coalition of Saraki Advocates for Atiku, COSAA, ta sha alwashin samar da kuri'u miliyan shida ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a yayin babban zaben kasa na badi.

Jagoran hadin kan kungiyar na kasa baki daya, Ola Kolawole, shine ya bayar da shaidar hakan a yau Alhamis cikin wata sanarwa yayin taron manema labarai da aka gudanar a babban birnin Ilorin na jihar Kwara.

Kungiyar yakin neman zaben Atiku ta sha alwashin samun kuri'u 6m a zaben 2019

Kungiyar yakin neman zaben Atiku ta sha alwashin samun kuri'u 6m a zaben 2019
Source: Facebook

A cewar Mista Kolawole, babbar manufar kungiyar ta takaita ne kadai wajen fafutikar tattaro mamakon kuri'u daga dukkanin jihohi 36 da ke fadin kasar nan ta hanyar yakin neman zabe na gida-gida da za ta kaddamar a kwana-kwanan nan.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar za ta zage dantsen ta wajen yabawa kwazon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, kasancewar sa jagoran yakin neman zabe na jam'iyyar PDP na kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Yadda gwamnatin tarayya ta ɓatar da $322m da ta kwato a hannun iyalan Abacha - Garba Shehu

Mista Kolawole ya kara da cewa, jagorancin Saraki ya girmama ta fuskar nagarta da kuma aminci gaske mai tabbatar da kwararar mamakon romo na dimokuradiyya da ko shakka ba bu ya cancanci yabo.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci Atiku da cewar da ana kan tsari na gaskiya da tuni ya fara hunhuna a gidan dan Kande.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel