Ba za mu yarda da kashe-kashen Zamfara ba, barazana ne ga damokradiyyarmu - Saraki

Ba za mu yarda da kashe-kashen Zamfara ba, barazana ne ga damokradiyyarmu - Saraki

- Shugaban majalisar dattawa, Saraki ya yi Allah wadai da kashe-kashen da ake a jihar Zamfara

- Ya bayyana lamarin a matsayin rashin imani, wanda ba za’a amince dashi ba

- Saraki yace hakan babban barazana ga damokardiyar kasarmu, musamman a yanzu da zabe ke dada gabatowa nan da yan kwanaki 50 masu zuwa

Shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya bayyana kashe-kashen da ake a jihar Zamfara a matsayin rashin imani, wanda ba za’a amince dashi ba sannan yayi kira ga hukumomin tsaro da su chanja dabaru domin kawo karshen mumunan halin da ake ciki.

Ba za mu yarda da kashe-kashen Zamfara ba, barazana ne ga damokradiyyarmu - Saraki

Ba za mu yarda da kashe-kashen Zamfara ba, barazana ne ga damokradiyyarmu - Saraki
Source: Depositphotos

Ya kuma bayyana kashe-kashen a matsayin babban barazana ga damokardiyar kasarmu, musamman a yanzu da zabe ke dada gabatowa nan da yan kwanaki 50 masu zuwa.

Saraki a wani jawabi dauke das a hannun babban hadiminsa, Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa halin da jihar Zamfara ke ciki abu ne sabanin 2015 da rikicin da aka fuskanta a yankin arewacin kasar ya kasance a yankin arewa maso gabas ne kadai, a yanzu arewa maso yamma ma ta zamo cike da jinin bayin Allah da basu ji ba basu gani ba.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari mace ce mai matukar mutunci – Kakakin Atiku

Yace kashekashen ya dauki tsawon lokaci kuma cewa lamarin bai samu kula yadda ya kamata ba da kuma manufar da ya kamata don kawo karshen shi.

Ya kara da cewa karara hakan alamu ne da ke nuna gazawa a cikin al’amarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel