Yadda gwamnatin tarayya ta ɓatar da $322m da ta kwato a hannun iyalan Abacha - Garba Shehu

Yadda gwamnatin tarayya ta ɓatar da $322m da ta kwato a hannun iyalan Abacha - Garba Shehu

A sakamakon tuhumar da 'yan adawa ke yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na almundahana da karkatar da kudaden da ta kwato daga hannun barayin gwamnati, a halin yanzu fadar shugaban kasa ta yi martani gami karin haske akan gaskiyar lamarin.

Babban hadimi na musaman ga shugaban kasa kan hulda da manema labarai da kuma al'umma, Mallam Garba Shehu, ya yi karin haske dangane da yadda gwamnatin tarayya ta gididdiba Dalar Amurka Miliyan 322 da ta kwato daga hannun iyalan tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, babban hadimin na fadar shugaban kasa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa a jiya Laraba cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Tsohon Shugaban kasa; Marigayi Janar Sani Abacha

Tsohon Shugaban kasa; Marigayi Janar Sani Abacha
Source: Getty Images

Mallam Shehu ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta rarraba wannan kudade ne ga mafiya talaucin al'ummar Najeriya, wajen biyan N5000 ga kimanin iyalai 300, 000 a fadin kasar nan karkashin shirin nan na Social Investment da gwamnatin tarayya ta assasa.

Ya ci gaba cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi wannan hobbasa ne bisa ga yarjewar gwamnatin kasar Switzerland inda marigayi Abacha ya yi ajiyar almundahanar sa a wani babban banki na kasar.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ba ya tausayin 'yan Najeriya - PDP

Wannan yunkuri na gwamnatin tarayya ya yi daidai da yarjejeniyar gwamnatin kasar Switzerland da kuma babban bankin duniya da a halin yanzu suka sanya idanun lura dangane da yadda gwamnatin Najeriya ke gudanar da shige da fice na kudaden.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jam'iyyar PDP ta yi gwamnatin tarayya da karkatar da akalar wannan kudade domin cimma kudirin ta na yakin neman zaben shugaban kasa Buhari a zaben kasa na badi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel