Shugaba Buhari ba ya tausayin 'yan Najeriya - PDP

Shugaba Buhari ba ya tausayin 'yan Najeriya - PDP

A yayin da ake ci gaba da kwarara matsananciyar adawa ta siyasa tsakanin manyan jam'iyyu biyu na kasar nan, jam'iyyar adawa ta PDP ya sake yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo kan al'amurran da suka shafi takakawan kasar nan.

Mun samu cewa jam'iyyar adawa ta PDP, ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin nuna wata damuwa kan jin dadin al'ummar Najeriya.

Jam'iyyar ta ke cewa, ba bu sauran tausayi ko jin kan talakawan Najeriya a zuciyar Buhari da ko shakka ba bu ba ya da wata damuwa ta halin kunci na rayuwa da suke fuskanta a yanzu.

Shugaba Buhari ba ya tausayin 'yan Najeriya - PDP

Shugaba Buhari ba ya tausayin 'yan Najeriya - PDP
Source: Twitter

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a jiya Laraba a babban birnin kasar nan na tarayya.

Ologbondiyan ya ce a halin yanzu an yi walkiya kuma al'ummar Najeriya sun fahimci rashin jin kan su da ya mamaye zuciyar Buhari. Hakan ya sanya ba su da wani zabi a babban zaben kasa n a badi face dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

KARANTA KUMA: Ka zargi kanka a kan rashin cimma nasarar yaki da rashawa - Atiku ga Buhari

Mista Kola ya hikaito yadda tsohon mataimakin shugaban kasa ya yiwa wata Marainiyar budurwa, Aisha Haruna, sha tara ta arziki da azal ta afkawa a garin Daura da ke jihar Katsina.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya yi kira ga hukumomi masu ruwa da tsaki kan gaggauta binciken iyalan Buhari da mallakar kamfanin sadarwa na Etisalat da ya sauya suna zuwa 9 Mobile da kuma bankin Keystone.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel