Rikicin Zamfara zai haifar da karancin abinci a Najeriya – Gwamnatin tarayya

Rikicin Zamfara zai haifar da karancin abinci a Najeriya – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta yi gargadi akan yiwuwar samun karancin abinci a fadin kasar sanadiyar munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke ci gaba da kai wa al’umman jihar Zamfara wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Ministan harkokin cikin gida, Laftanar Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya ya yi gargadin a yayin da ziyarci jihar domin tantance girmar barnar ‘yan bindigar suka yi a fadin jihar.

Dambazau ya ce, mafi akasarin wadanda hare-haren ke shafa, manoma ne, abin da ya ce, zai iya haddasa mummunar illa ga harkar noma da samar da abinci a kasar.

Rikicin Zamfara zai haifar da karancin abinci a Najeriya – Gwamnatin tarayya

Rikicin Zamfara zai haifar da karancin abinci a Najeriya – Gwamnatin tarayya
Source: Facebook

Ministan ya yi wa ‘yan bindigar kashedin karshe tare da fadin cewa, gwamnatin tarayya ta bullo da wasu dabaru masu tsauri don murkushe su.

KU KARANTA KUMA: Kalaman kiyayya: CAN ta gargadi El-Rufai akan hukunta Fasto Enenche

A bangare guda, Ministan Tsaron Kasar, Mansur Dan Ali, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa, dakarun sojin kasar sun kashe mutane da dama da ke zanga-zangar adawa da hare-haren ‘yan bindigar a ranar Kirismati a jihar ta Zamfara

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel