2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari

2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari

- Kungiyar magoya bayan Buhari a mazabar Sarkin Yara A Ward da ke Daura, ta fara wayarwa masu zabe kai

- Hakan na daga cikin kokarinsu na ganin Buhari da Masari sun zarce a 2019

- A cewar kungiyar ya kamata a bari Buhari kammala ayyukan ci gaba da yake kan yi a kasar

Kungiyar magoya bayan Buhari a mazabar Sarkin Yara A Ward da ke Daura, ta fara wayarwa masu zabe kai a kokarinsu na ganin tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari a 2019.

Shugaban kungiyar, Malam Ali Dahiru-Daura ya fadama kamfanin dillancin labarai a Daura a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba cewa sun fara bin gida-gida, kauye-kauye da gari-gari don wayarwa mutane kai a Daura, Baure, Sandamu, Maiadua da Zango don tabbatar da cewa shugabannin biyu wato Buhari da Masari sun yi nasara.

2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari

2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa gwamnatin Buhari a shekaru uku da rabid a tayi tana mulki ta kawo sauyi sosai musamman ga tattalin arzikin kasa, inda ya kara da cewa martabar Najeriya wanda ta rasa a baya sun dawo musamman a kasashen duniya.

Dahiru-Daura ya ci gaba da cewa gwamnatin ta gina daruruwan hanyoyi da tashoshin jiragen kasa a fadin yankunan kasar guda bakwai, inda ya kara da cewa a yanzu a rayar da sufurin jirgin kasa.

KU KARANTA KUMA: Babu wasu jami’ai da suka tsere kan yaki da Boko Haram – Hukumar yan sanda

Yace akwai bukatar yan Najeriya su sake zabar Buhari domin ya samu damar ci gaba da ayyukan ci gaba da ya soma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel